Boko Haram sun yi kwanaki 3 su na ta’adi a Yobe, ba a san inda Gwamnan jihar ya shiga ba
- ‘Yan ta’addan Boko Haram sun hargitsa karamar hukumar Geidam a Yobe
- Har yanzu babu wanda ya san inda Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya shiga
- Tun ranar Juma’a sojojin Boko Haram su ka shiga kauyen tsohon Gwamnan
Babu wanda ya san takamaimen inda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shiga a halin yanzu. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.
Tun da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram su ka kai hari a garin Geidam a ranar Juma’a, 23 ga watan Afrilu, ba a san inda gwamnan ya shiga ba.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar gwamna Mala Buni ya na babban birnin tarayya Abuja inda ya saba zama, ko kuma ya na Damaturu.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta ce kashe Idris Deby zai ‘taba’ Najeriya sosai
Mafi yawan lokuta Mai Mala Buni ya na zama ne a garin Abuja saboda harkokin jam’iyyar APC wanda yanzu haka shi ne shugabanta na rikon kwarya.
Daga ranar Juma’a zuwa yanzu, mutanen garin Geidam su na ta faman wasan tsere da ‘yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini jama’an a yankin.
Bayan dakarun sojoji sun yi wa ‘yan ta’addan luguden wuta, abubuwa sun soma lafa wa, amma daga baya mayakan na Boko Haram su ka sake dawowa.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, ya bayyana cewa ana jinyar wasu daga cikin wadanda su ka yi rai a harin.
KU KARANTA: Duk Sarkin da ya yi sake aka mutane, zai rasa sarautarsa a Imo
Kamar yadda Dr. Mohammed Goje ya bayyana, mai girma gwamna ya bada umarni a kai wa wadanda ‘yan ta’addan su ka kai wa hari, agajin gaggawa.
An hallaka mutane da-dama a garin Geidam, har wani mutumin yankin ya shaida wa ‘yan jarida cewa lamarin ya kai yadda ba za a iya yi wa gawa jana’iza ba.
A halin yanzu, mutane su na tsere wa ne daga wannan gari da ya na cikin manyan garuruwan Yobe.
Dazu an ji labari cewa dakarun Boko Haram su na ruwan wuta a garin Mainok dake da nisan kilomita 60 zuwa babban birnin jihar Borno watau Maiduguri.
Mainok ce hedkwatar karamar hukumar Kaga dake Borno a arewa maso gabas. Sojojin Boko Haram su na ta bankawa gidajen jama'a wuta, su na fasa shaguna.
Asali: Legit.ng