Chad: Gaba ta shiga tsakanin ‘Yan gida-daya da Sojoji kwana 2 bayan an birne Idriss Deby

Chad: Gaba ta shiga tsakanin ‘Yan gida-daya da Sojoji kwana 2 bayan an birne Idriss Deby

- Mutuwar Idriss Deby ta bar kura a kasar Chadi a kan wanda zai gaji kujerar sa

- Ba a ga maciji tsakanin manyan ‘ya ‘yan marigayi Idriss Deby da matan aurensa

- ‘Yan adawa da bangaren sojoji da mutanen gari ba su goyon bayan mulkin Soji

Kwanaki biyu da birne shugaba Idriss Deby a kasa, jaridar Daily Trust ta ce an samu sabani tsakanin manyan siyasar kasar da ‘yanuwan marigayin.

Inda rigimar farko take shi ne wasu daga cikin ‘yan dangin marigayin ba su son ganin Janar Mahamat Idriss Déby ya matso kusa da kujerar shugaban kasa.

Rahotanni sun ce akwai sabani tsakanin Mahamat Idriss Déby da ‘dan ubansa, Zakaria Idriss Déby. Sannan babu jituwa tsakanin 'ya 'yan da matan mahaifinsu.

KU KARANTA: Kasashe 9 da Iyaye su ka mutu, su ka bar ‘Ya ‘yan cikinsu kan mulki

Hinda Déby ce wanda ta yi fice a matan marigayin ita ce ta ke da ta-cewa a gwamnati. Mutuwar maigidanta, ya sake fito da rigimar da ke tsakaninta da ‘yayansa.

Akwai wannan matsala a gidan soja yayinda sojoji su ka karbe mulki kuma ake shirin yin zabe bayan farar hula sun dade su na rike da kasar ta hannun Idriss Deby.

Jam’iyyun adawa sun yi kaca-kaca da matakin da aka dauka na nada Mahamat Déby a matsayin shugaban rikon kwarya, su ka ce juyin-mulkin cikin gida aka yi.

Haka zalika kungiyar AU ta kasashen Afrika ta bukaci sojoji su sallama wa farar hula mulki a Chadi.

KU KARANTA: Da gaske an hallaka Mahamat Idriss Déby bayan ya hau mulki?

Chad: Gaba ta shiga tsakanin ‘Yan gida-daya da Sojoji kwana 2 bayan an birne Idriss Deby
Marigayi Idriss Deby
Asali: Twitter

Da alamu duk abin da ya ke ta faru wa, Faransa wanda ta raini Chadi da wasu kasashen yankin, ba ta adawa ga Mahamat, da sunan goyon bayan zaman lafiya.

A halin yanzu, kungiyoyin kasuwanci sun kira gagarumin yajin-aiki, yayin da ‘yan tawayen FACT su ka ja-kunnen gwamnati cewa ba mulkin gado ake yi a kasar ba.

A doka da tsarin mulkin Chadi, shugaban majalisa ne ya ke da ikon ya karbi mulki, ya shirya sabon zabe a duk lokacin da aka samu shugaban kasar ya mutu.

Bayan rasuwar Idriss Déby ba haka aka yi ba, domin ‘dan cikinsa, Mahamat Idriss Déby, aka dauko, aka kakaba a matsayin sabon shugaban kasa na rikon kwarya.

Mahamat Deby zai jagoranci kasar Afrikar na tsawon watanni 18 yayin da sojoji za su gudanar da zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel