Ya isa haka: Jam’iyyar APC ba ta goyon-bayan Gwamnatin Buhari ta sake kara kudin man fetur

Ya isa haka: Jam’iyyar APC ba ta goyon-bayan Gwamnatin Buhari ta sake kara kudin man fetur

- Matakin da jam’iyyar APC ta dauka shi ne a bar farashin mai ya tsaya cak

- Jam’iyyar ba za ta so a kuma kara farashin lita a gidajen man Najeriya ba

- John James Akpanudoedehe ne ya bayyana matsayar Jam’iyyar kwanan nan

Jaridar Daily Trust ta ce matsayar jam’iyyar APC mai mulki a halin yanzu shi ne ka da gwamnatinta ta sake a yi wani karin farashin man fetur.

Rahoton ya ce wannan matsaya da jam’iyyar APC ta dauka ya jawo abin magana a kasar nan.

Sau shida shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi karin farashin kudin man fetur tun bayan da ya karbi mulki daga hannun Dr. Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: 'Yan kasuwa sun ce ya kamata litar man fetur ya kai N200

Sakataren rikon kwarya na kasa na APC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce sun tsaida cewa jam’iyya ba ta goyon bayan wani karin farashi.

Rahotanni sun tabbatar da a zaman da aka yi da Yemi Osinbajo, an tsaida maganar cewa gwamnatin tarayya ba za ta tashi kudin man fetur ba.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sun cin ma wannan matsaya ne a taron da aka yi da manyan gwamnati da jiga-jigan jam’iyyar APC.

Wadanda aka yi wannan zama da su sun hada da SGF, Boss Mustapha, Farfesa Ibrahim Gambari, Ahmad Lawan, Ovie Omo-Agege da Abubakar Malami.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta zauna a kan maganar farashin wuta da mai

Ya isa haka: Jam’iyyar APC ba ta goyon-bayan Gwamnatin Buhari ta sake kara kudin man fetur
Shugaban kasa Buhari da Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Wasu daga cikin shugabannin rikon kwarya na APC su na wajen wannan taro kamar yadda John James Akpanudoedehe ya bayyana a matsayin jam’iyyar.

Kafin a kafa wannan kwamiti da zai duba batun tsaida farashin mai a kasar nan, sai da shugaban APC na riko, Mai Mala Buni ya zauna da shugaban kasa.

Amma wasu masana su na ganin APC ta dauki wannan matsaya ne don siyasa, domin ta burge talakawa saboda kwadayin kuri’arsu a zabe mai zuwa.

Tun tuni gwamnan nan ta ke wakar cewa ta cire tallafin mai. Amma jiya aka ji gwamnatin Muhammadu Buhari ta na cacar N4.6bn a kowace rana.

Alkaluma sun nuna ana kashe N216 yanzu kafin litar man fetur ya kai gidan mai. Amma farashin fetur bai canza a gidajen mai ba tun karshen shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel