Chad, da kasashe 8 da Iyaye su ka mutu, su ka bar ‘Ya ‘yan cikinsu kan mulki a Afrika

Chad, da kasashe 8 da Iyaye su ka mutu, su ka bar ‘Ya ‘yan cikinsu kan mulki a Afrika

Masu karatu sun san a nahiyar Afrika ba bakon abu ba ne a ga shugaban kasa ya mutu, sannan ‘dan sa ya gaji kujerar shugaban kasar.

21st Century Chronicle ta zakulo jerin shugabannin kasashe tara a Afrika da ‘ya ‘yansu su ka dare kan karagar mulki bayan sun bar Duniya.

A cikin wannan jeri za a ga cewa a kasashe shida, kai-tsaye ‘ya ‘yan tsofaffin shugabanni su ka hau kan kujerar mulki bayan mahaifansu.

A Kenya, Mauritius da Bostwana, ‘ya ‘yan sun bi sahun mahaifansu ne shekaru bayan sun bar mulki.

Ga shugabannin nan kamar haka:

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya girgiza da labarin mutuwar Deby

1. Faure Gnassingbé Eyadema – kasar Togo

A 2005 ne Faure Gnassingbé Eyadema ya zama shugaban kasar Togo bayan rasuwar mahaifinsa watau shugaba Gnassingbé Eyadema wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 38.

2. Joseph Kabila – kasar Kongo

Joseph Kabila ya bi tafarkin Lawrence Kabila wanda aka kashe yayin da yake mulkin Kongo. Kabila ya na shekara 30 ya dare kan mulki, ya yi shekara 18 ya na shugabanci.

3. Ali Bango – kasar Gabon

Bayan rasuwar Omar Bongo Ondimba a 2009, ‘dansa Ali Bongo ne ya zama sabon shugaban kasa. Tun 1967 har zuwa yanzu, ‘yan gidan bango ne su ke shugabanci a kasar Gabon.

4. Sarki Mohammed na 6 – kasar Maroko

Tun shekarar 1999, Sarki Mohammed na shida ya zama shugaban kasar Maroko ya na shekara 36. Mai martaban ya samu mulki ne bayan mutuwar mahaifinsu, Sarki Hassan II.

5. Ian Khama – kasar Botswana

Tsakanin 1966 zuwa 1980, Seretse Khama ya mulki kasar Botswana. Shekaru kusan 30 bayan ya bar mulki, ‘dan cikinsa, Ian Khama ya zama shugaban kasa ya na da shekara 55.

Chad, da kasashe 8 da Iyaye su ka mutu, su ka bar ‘Ya ‘yan cikinsu kan mulki a Afrika
Idriss Deby da sabon Shugaban Chad, Mahamat Deby
Asali: Twitter

KU KARANTA: Lokacin da Idris Deby ya jagoranci Sojoji har cikin Sambisa

6. Uhuru Kenyatta – kasar Kenya

Shekara 35 bayan mutuwar shugaban Kenya na farko, Jomo Kenyatta, Uhuru Kenyatta ya zama shugaban kasa. Uhuru ya na karamin yaro a lokacin da mahaifinsa ya yi mulki.

7. Navin Ramgoolam – kasar Mauritius

A 1985 tsohon shugaban Mauritius, Dr. Seewoosagur Ramgoolam ya rasu. Tsawon shekaru bayan ya bar kan mulki, aka sake ‘dansa Navin Ramgoolam a matsayin shugaban kasa.

8. Mswati III – Eswatini

Mai martaba Mswatti III ya hau gadon sarauta a 1986 ya na ‘dan shekara 18. Mswatti III ya gaji mahaifinsa, Sobhuza II, wanda ya yi shekaru fiye da 80 ya na rike da Swaziland.

9. Mahamat Deby Itno – kasar Chad

Na karshe a jerin shi ne Mahamat Idriss Deby Itno wanda ya gaji mahaifinsa ya na ‘dan shekara 37. Sabon shugaban kasar Chadin ya hau kujerar da Idriss Deby Itno ya dade a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel