Da duminsa: Yan bindiga sun kashe dalibai 3 cikin wadanda suka sace a Jami’ar Greeenfield Kaduna

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe dalibai 3 cikin wadanda suka sace a Jami’ar Greeenfield Kaduna

- Kwanaki uku bayan garkuwa da su, an tsinci gawawwakinsu a cikin daji

- Gwamnan jihar Kaduna ya yi Alla-wadai da wannan kisan gillan da aka yiwa dalibai

- Wannan ya biyo bayan kisan ma'aikacin jami'ar guda daya a ranar da akayi garkuwan

Yan bindigan da suka kai hari jami’ar GreenField dake Kaduna inda sukayi awon gaba da dimbin dalibai sun bindige mutum 3 cikin daliban da suka sace.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki ranar Juma’a.

An tsinci gawawwakin daliban uku ranar Juma’a a kauyen Kwanan Bature, dake kusa da jami’ar, Aruwan ya kara.

"Cikin wani halin rashin tausayi da mugunta, yan bindigan da suka sace daliban jami'ar Greenfield sun bindige dalibai 3," yace.

"An tsinci gawawwakin daliban uku yau (Juma'a) a kauyen Kwanan Bature, wani waje dake kusa da jami'ar kuma kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida da kwamandan Operation Thunder Strike, Lt.Col. MH Abdullahi sun kai gawawwakin dakin ajiye gawawwaki."

"Gwamna El-Rufa'i ya yi Alla-wadai da kisan wadannan daliban uku kuma ya siffanta matsayin mugunta.. Ya ce yan bindiga sun zama ashrarun mutane kuma ya wajaba a yakesu bisa zaluncinsu."

KU DUBA: Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe dalibai 3 cikin wadanda suka sace a Jami’ar Greeenfield Kaduna
Da duminsa: Yan bindiga sun kashe dalibai 3 cikin wadanda suka sace a Jami’ar Greeenfield Kaduna
Asali: Original

KU KARANTA: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Mun kawo muku cewa yan bindigan da sukayi awon gaba da daliban jami'ar Greenfield a jihar Kaduna sun bukaci a basu kudi milyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sake daliban.

A cewar rahoton TheNation, yan bindigan sun yi barazanar kashe daliban idan ba'a biya kudin ba. Majiyoyi sun bayyana cewa adadin daliban da aka sace na tsakanin 17 da 23; kimanin mata 14 da maza takwa.

An samu labarin cewa yanzu haka an kaddamar da tattaunawa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng