Caccakar Gwamna Ganduje ya jefa rayuwar Hadimar Gwamnatin Kaduna a mugun hadari

Caccakar Gwamna Ganduje ya jefa rayuwar Hadimar Gwamnatin Kaduna a mugun hadari

- Sai’da Saad Bugaje ta soki yadda Gwamnan Kano ya fara yaki da Coronavirus

- A dalilin wadannan maganganu da wannan mata ta yi, ta samu kanta a matsala

- Bugaje wanda ta ke aiki da Gwamnatin Kaduna ta ce ta na fuskantar barazana

Wata Lauya kuma mai ba gwamnatin Kaduna shawara, Sai’da Saad Bugaje, ta samu kan ta a cikin matsala bayan ta takalo gwamna Abdullahi Ganduje.

HumAngle ta ce Sai’da Saad Bugaje ta shiga halin ha’ula’i ne tun da ta soki yadda gwamnatin Kano ta ke yaki da annobar cutar COVID-19 a 2020.

Tattaunawar wannan Baiwar Allah da wasu na-kusa da ita ya fito fili inda aka ji ta na sukar rawar da shugabanni su ke taka wa wajen kauda cutar.

KU KARANTA: Mu na cikin hadarin katutun bashi a Najeriya – Sanusi II

A cewar Bugaje, jihar Kano ta yi sake a lokacin da annobar ta shigo, lokacin da gwamna Abdullahi Ganduje ya nemi gwamnatin tarayya ta ba shi gudumuwa.

“Na kuma ce dangin gwamna ne su ke mulkar jihar Kano, da su ake yin komai. A karshe maganar ta wa ta fita, kuma ban ga komai a kan wannan ba", inji ta.

Sai’da Saad Bugaje ta shaida wa jaridar cewa ba za ta yi tsit a lokacin da abubuwa ba su tafiya ba daidai a kasa ba, ta ce sukar shugabanni ba bakon abu ba ne.

Bayan ta caccaki gwamnan Kano sai kwatsam wasu su ka dura gidan ta a watan Satumba su na neman su ganta, ta ce mutanen sun yi basaja ne da kayan gida.

KU KARANTA: Rigima ta kare a PDP, Ayo Fayose ya ba marada kunya, ya ajiye kayan fada

Caccakar Gwamna Ganduje ya jefa rayuwar Hadimar Gwamnatin Kaduna a mugun hadari
Sai’da Saad Bugaje da Gwamna Ganduje Hoto: Hum Angle/This Day
Asali: UGC

Da Sai’da Saad Bugaje ta nemi jin su wanene wadannan mutane, sai su ka hakikance a kan cewa manyan kasar ne su ka aiko su daga Kano domin su zauna da ita.

Ganin cewa akwai yiwuwar wadannan mutane ‘yan bindiga ne, Sai’da Saad Bugaje ta yi maza ta boye ‘ya ‘yanta, ta rufe gida, ta bukaci a aiko mata jami’an tsaro.

Wannan mata ta ce dole ta je kotu ta bukaci a hana gwamnatin Kano cafke ta. Bugu da kari, rayuwarta da ta ‘ya ‘yanta da ke makaranta na fuskantar barazana.

A baya kun samu rahoton cewa jam'iyyar PDP ta bayyan abin da ta ke yi a kan rigimar Rabiu Kwankwaso, Aminu Wali, da gwamna Aminu Tambuwal da sauransu.

Manyan PDP za su dinke barakar da aka samu tsakanin mabiya Kwankwasiyya da magoya-bayan Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a kan zaben jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel