Gandollar: Sai mun kunyata wadanda suka kulla min sharri, Ganduje
- Bayan shekaru biyu, gwamna Ganduje ya yi martani kan bidiyoyin dala
- Gwamnan Kano ya shigar da gidan jaridar da ta wallafa bidiyon kotu
- Har yanzu kotu bata yanke hukunci ba yayinda gwamnan ke jaddada cewa bidiyon bogi ne
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sake jaddada cewa bidiyon da ya bayyana a 2018 yana cusa dalolin Amurka cikin aljihunsa sharri ne kuma na boge ne.
Jaridar Daily Nigerian a 2018 ta wallafa bidiyoyin kuma hakan ya yi matukar batawa gwamnan suna.
Bayan shekaru biyu, Ganduje ya bada amsa kan wannan lamari a shirin BBC Hausa "A fada a cika" wanda gidauniyar MacAuthur ke daukar nauyi.
Ganduje ya ce bidiyon na bogi ne kuma "wadanda suka yi za su ji kunya."
"Babu shakka wannan bidiyo karya ne kuma muna nan muna shirye-shirye amma ba zamu fadi irin shirin da muke ba...duk wadanda suka sa hannunsu a wannan lamari za su ji kunya," cewar Ganduje.
KU KARANTA: Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da tasiri, in ji Gwamna Ganduje
Kalli bidiyon:
KU KARANTA: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu
Mun kawo muku cewa karar bidiyon daloli tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar, a ranar Litinin ta dauka sabon salo.
Wanda yayi karar ya bukaci hutun kotu domin gyara karar da sauran ikirarin da yayi a gaban kotun.
Ganduje ya maka mawallafin da wasu a gaban wata babbar kotun jihar Kano inda yake bukatar a biya shi N4 biliyan na bacin suna sakamakon wani bidiyo da ya bazu.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng