Danyen mai ya kara kudi a Duniya, farashin litar man fetur ya na neman kaiwa N220
- Ana kashe N216 yanzu kafin litar man fetur ya kai gidan mai a Najeriya
- Amma farashin man fetur bai canza a gidajen mai tun Disamban 2021 ba
- Idan aka yi lissafi, gwamnati ta na kashe fiye da Biliyan 4 a tallafin fetur
Jaridar Punch ta rahoto cewa kudin da ake kashe wa wajen shigo da Premium Motor Spirit watau man fetur ya tashi zuwa N216.31 a kan kowace lita guda.
Rahoton ya bayyana cewa an samu karin kudin ne a sakamakon canjin da aka samu na farashin danyen mai da kuma tashin da dalar Amurka ta yi kwanaki.
A watan Maris, hukumar PPPRA ta fitar da jadawalin da ya nuna ya kamata farashin litar man fetur ya na tashi tsakanin N209.61 zuwa N212.61 a gidan mai.
KU KARANTA: Ana bincike a kan abin da ya jawo mana gobara a jihar Kano - INEC
Duk da sauyin da aka samu, farashin mai bai canza daga N165 tun watan Disamban shekarar 2020 ba.
A yanzu farashin sarin fetur ya kai N239.31, alhali abin da ake saida man ya na tsakanin N162-N165, kenan ana samun gibin kusan N80 a kan kowace lita.
Kowace ranar Duniya, NNPC ta na ikirarin ana batar da lita miliyan 60 na man fetur. Hakan ya na nufin ana kashe N4.64bn a kan kudin tallafin fetur a kullum.
KU KARANTA: PDP ta ki karbar uzurin tsohon Gwamnan Neja, ta dakatar da shi
Kudin da ake kashe wa wajen shigo da fetur sun hada da kudin dako (N4.81), kudin da hukumomin NPA, NIMASA (N2.49, N0.23) su ke karba, da kudin adana (N2.58).
Wajen lissafin kudin litar fetur, hukumomi su na auna kudin sari, kudin aiki, kudin zirga-zirga.
Duk da gwamnati ta na cewa ta raba kan ta da abin da ya shafi farashin fetur, kamfanin mai na kasa watau NNPC ne aka dogara da shi wajen shigo da kayan mai.
A baya kun ji cewa danyen mai ya na ta kara tsada a kasuwannin Duniya. 'Yan kasuwa su na ganin cewa ya kamata litar mai ta kai N200 a halin da ake ciki.
Jam'iyyar hamayya ta PDP ta ce sam bai kamata farashin litar mai ya wuce Naira 70 ba. PDP tayi kira ga gwamnatin APC ta tsaida farashi ta yadda za a samu sauki.
Asali: Legit.ng