Shehin Malamin Musulunci ya bayyana wasu dalilai 3 da ya sa aka taso Isa Pantami a gaba
- Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya kare Isa Ali Pantami daga zargin ta’addanci
- Babban Malamin ya fadi abubuwan da su ka jawo ake yi wa Ministan ‘sharri’
- Shehin ya ce an yaudari Musulman da su ka shiga sahun masu sukar Ministan
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto mni, ya tsoma bakinsa game da abin da ke faruwa da Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami.
Da yake karatun tafsirin da ya saba yi a masallacin Abu Hurairah da ke Polo Club a garin Sokoto, malamin ya fadi abin da ya sa aka taso Ministan a gaba.
A cewar sa, ana neman hana Isa Pantami sakat ne saboda an ga kokarin da yake yi, sannan ga ficen da ma’aikatarsa ta yi, kuma ana masa kallon shehi.
KU KARANTA: Pantami: Abdullahi Bala-Lau ya wanke Ministan sadarwa da hujjoji
“Dama ai ba za ku yi tsammanin ya shiga irin wannan kara-kara, kuma ya yi aiki, ana ganin ma’aikatarsa a cikin wanda ta yi fice, a matsayin malamin addini a kyale sa haka ba.”
“Ba zai yi nasara a kyale shi ba, ba zai yiwu ba. To, sai an yi ta hakuri” inji Farfesa Sokoto kamar yadda wani bidiyo da aka wallafa jiya a shafin Twitter ya nuna.
Malamin ya ce: “Kafin wannan ai an kula masa wasu sharrin; an ce ya saye manyan gidaje a Abuja." Ya ce idan ma ya saye gidajen, ya kai matsayin mallakarsu.
Ya cigaba: “Yanzu wanda aka kulla, wai ya na tare da ‘Yan Boko Haram. Mutumin da ya saida rayuwarsa a lokacin da kowa ke tsoron ya zauna da Mohammed Yusuf.”
KU KARANTA: Babu abin da ya hada Pantami da kisan Patrick Yakowa – Shugaban CAN
Mansur Sokoto ya ce sa’ilin da tsohon shugaban Boko Haram, Mohammed Yusuf, ya zo Sokoto, ya nemi ya yi zama da shi sau uku, amma sam ya ki bari su hadu.
“Mutumin da ya sayar da rayuwarsa, ya karantar da mutane gaskiya a kan ta’addanci, yau shi ake jingina wa ta’addanci." Farfesan ya na mai fallasa shirin da ake yi.
“Ku sani ba da Isa (Pantami) su ke ba, ba da kujerarsa su ke ba. A’a, da musulunci. su ke yi.” Shehin ya yi tir da musulman da su ka bi sahun sukar, ya kira su wawaye.
A jiya kun ji shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya yi fatali da yunkurin kiran a sauke Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Gbajabiamilla ya fadi dalilin da ya sa Majalisa ta ki tattaunawa game da dambarwar Ministan, ya ce amma ba a hana kowa ya bijiro da kiran a tsige Sheikh Pantami ba.
Asali: Legit.ng