Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin sallamar Dr Isa Ali Pantami

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin sallamar Dr Isa Ali Pantami

Majalisar wakilan tarayya ta yi waje da kudirin wani dan majalisa wanda ya bukaci a sallami kuma a binciki Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, kan zargin alaka da yan ta'adda.

Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Ndudi Elumelu, a ranar Laraba, ya yi kira ga majalisa ta bukaci ministar sadarwan yayi murabus ko kuma sallamesa saboda goyon bayan yan ta'addan a shekarun baya.

A zauren majalisan, Elumelu ya ce gabatar da kudirin cewa Pantami yayi murabus ko a sallamesa, Punch ta ruwaito.

Amma Kakakin majalisar wakilan, Femi Gbajabiamila, ya dakatar da shugaban marasa rinjayen inda yace kudurinsa ba ta da alaka da huruminsa matsayin dan majalisa.

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin sallamar Dr Isa Ali Pantami
Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin sallamar Dr Isa Ali Pantami
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel