Kungiyar Izala ta bada hujjoji masu karfi da za su wanke Sheikh Pantami daga zargi
- Kungiyar Izala ta yi magana game da tirka-tirkar da aka jefa Sheikh Isa Pantami
- Shugaban Izala ya bayyana cewa babu abin da ya hada Ministan da ta’addanci
- Abdullahi Bala Lau ya ce Isa Pantami ya cancanci a yaba wa kokarin da yake yi
Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah ta yi tir da danganta Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami da ta’addanci.
Shugaban Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah na JIBWIS, Abdullahi Bala Lau ya bayyana zargin da ake yi wa Ministan kasar da furofaganda.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce miyagu ne su ke yada wannan jita-jita domin a bata wa Ministan suna.
KU KARANTA: FBI ta yi magana game da zargin dangantakar Pantami da Boko Haram
JIBWIS ta ce babu burbushin gaskiya a zargin da ake yi wa Ministan saboda dalilai kamar haka:
1. Dr. Isa Ali Pantami fitaccen malamin musulunci ne wanda ya kware wajen yada addinin da aka sani da zaman lafiya, ba ya goyon bayan ta’addanci ko zubar da jini.
2. Wadanda su ka san Dr. Isa Ali Pantami, sun san yadda ya tsaya tsayin-daka wajen yaki da ta’addanci. Za a ga haka a mukabalarsa da Muhammad Yusuf inda ya rika kafa masa hujjoji daga nassoshi. Akwai bidiyoyi da sauti da za a iya gani a kan wannan.
3. Namijin kokarin da Dr. Pantami ya yi a ma’aikatar sadarwa abin a yaba ne, ya yi kokarin maganin matsalar rashin tsaro, har ‘yan ta’adda su na barazanar hallaka shi.
KU KARANTA: PDP ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan sadarwa, ya wanke kan shi
4. Bayan haka, Pantami ya yi maganin asarar da gwamnati ta ke yi, ya jawo gwamnati ta adana kudi a bangaren sadarwa da fasahan zamani, an samu kudin-shiga.
Bala Lau ya ce wadanan su na cikin kokarin da Ministan ya yi, har ya na zargin ana kokarin a yaki musulunci ne da malaman addinin da su ka samu babban matsayi.
Shugaban kungiyar addinin ya jefa alamar tambaya, ya ce ko kuwa wasu ne su ke adawa da dabarun da Ministan ya kawo na inganta sha’anin sadarwa a Najeriya.
Kafin yanzu kun ji cewa jam'iyyar hamayya PDP ta ce babu dalilin da zai sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da zama da Ministan sadarwa na kasa.
PDP tace saboda waɗannan raɗe-raɗin da ke yawo a kan alakar Ministan da 'yan ta'adda, babban abin da ya kamata Dr. Isa Ali Pantami ya yi, shine ya ajiye muƙaminsa.
Asali: Legit.ng