Lokacin da Marigayi Deby ya kusa jefa hadimin Shugaban kasa Buhari a katuwar matsala

Lokacin da Marigayi Deby ya kusa jefa hadimin Shugaban kasa Buhari a katuwar matsala

A makon nan ne Marshal Idriss Déby Itno ya mutu wajen kare kasar Chadi da ya yi shekaru sama da 30 ya na mulki, tun da ya yi juyin-mulki a 1990.

Jaridar Daily Trust ta fitar da dogon rahoto inda ta yi karin bayani a game da Idriss Déby Itno, ta fadi abubuwan da ba a sani ba a kan tarihin marigayin.

Dodon Boko Haram

A 2015 Idriss Déby Itno ya yi ikirarin ya san inda shugaban Boko Haram yake. Marigayin bai yi nasarar kama Abubakar Shekau ba, amma ya yi masa lahani.

Bayan Deby ya jagoranci sojojinsa zuwa mafakar ‘yan ta’adda, ya yi masu barna, sai da Abubakar Shekau ya fitar da wani sako ya na tsine wa marigayin albarka.

KU KARANTA: Da gaske an hallaka Mahamat Idriss Deby Itno?

Jefa Ibrahim Gambari a matsala

Farfesa Ibrahim Gambari ya samu halartar wani biki na Idriss Déby, a lokacin hadimin shugaban kasar ya na aikin jakadancin kungiyar UN da AU a kasar Sudan.

Wasu sun soki yadda Ibrahim Gambari ya tsoma kansa cikin harkar shugaban kasar. An yi ta sukarsa a kan wannan a lokacin da Buhari ya ba shi mukami.

‘Dan Makiyaya ya zama Shugaban kasa

An haifi Déby ne a wani kauye da ake kira Berdoba da ke kusa da Fada. Mahaifinsa talaka ne wanda yake kiwon dabbobi. Amma a karshe ya zama shugaban kasa.

Marigayi Déby ya koyi karatun Kur’ani a Tine, kafin ya tafi makarantar Lycée Franco-Arabe ta garin Abeche, daga nan ne ya je ya yi digirinsa a jami’ar da ke Bongor.

Lokacin da Marigayi Deby ya kusa jefa hadimin Shugaban kasa Buhari a katuwar matsala
Idris Deby da sauran Shugabannin Afrika Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Idris Deby da ya yi shekara 30 ya na mulkin Chad

Horo a karkashin Muammar Gaddafi

Marigayi shugaban kasar Libya, Muammar Gaddafi, ya ba Déby gudumuwa. Shugaban Chadin ya samu horo a makarantarsa ta World Revolutionary Center.

Cibiyar World Revolutionary ta rika horas da matasa a kasar Libya. A nan ne Marshal Idriss Déby Itno ya kware wajen harkar amfani da manyan makamai.

A baya kun samu rahoto cewa Idriss Deby namijin Duniya ne. Deby, ya taba kutsawa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa a shekarar da ta wuce.

Deby ya shiga cikin rundunar da aka yi wa lakabi da “Operation Wrath of Bomo” da ta kutsa Sambisa a sakamakon hallaka wasu sojojin Chad da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng