Tuna-baya: Lokacin da Idris Deby ya jagoranci Sojoji har cikin kungurmin jejin Sambisa
- Idris Deby ya taba shiga cikin dajin Sambisa tare da wasu Sojojin kasar Chadi
- Marigayin ya nuna bajinta a lokacin da ya kutsa inda Boko Haram su ke fake
- A karshe Deby ya mutu bayan wasu ‘Yan tawayen Chadi sun harbe shi a kugu
Marigayi Idriss Déby ya kasance jan wuya, maras tsoro a rayuwarsa. A ranar Talata aka bada sanarwar kashe tsohon shugaban na kasar Chad.
‘Yan ta’addan kasar Chadi ne su ka yi sanadiyyar mutuwar Idriss Déby. Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa sun harbe shi ne a kwankwasonsa.
Daily Trust ta iya tuna cewa kusan shekara guda da ya wuce ne Deby ya jagoranci dakarun sojoji zuwa babban mafakar Boko Haram na Sambisa.
KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Idris Deby da ya yi shekara 30 ya na mulkin Chad
Deby ya shiga cikin rundunar da aka yi wa lakabi da “Operation Wrath of Bomo” da ta kutsa Sambisa a sakamakon hallaka wasu sojojin Chad.
Tsohon shugaban kasar ya tashi da kansa ya shiga jejin ne bayan Chadi ta rasa sojoji 90 a hannun ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram da ake yaki da su.
Ya ce: “Mun kaddamar da “Wrath of Bomo”. Dole mu kawo karshen ta’addanci domin mutanenmu, musamman na yankin tafkin Chadi su zauna lafiya.”
“Wannan shi ne makasudin yakin da mu ke yi da Boko Haram.” Deby ya fada a Twitter a lokacin.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun bukaci a biya N20m kafin su fito da Basaraken Ekiti
Bayan wannan namijin kokari da Deby ya yi, sojojinsa sun dura yankin Kelkoua da Magumeri.
A sanadiyyar hare-haren da sojojin Chadi a karkashin shugaban kasarsu, su ka kai, sun yi nasarar ruguza wuraren buyan Boko Haram, su ka karbe makamansu.
Bugu da kari, Deby da mutanensa sun cafke wasu sojojin Boko Haram, daga ciki har da manyan jagororin ‘yan ta’ddan. Wannan ya faru ne a cikin shekarar 2020.
A ranar Talata kun samu labari cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kadu wa da girgiza bisa mutuwar shugaban kasar Chadi, Idris Deby.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mutuwar Deby za ta haifar da gurbi a yakin da ake yi da 'ya ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabas da iyakokin yankin.
Asali: Legit.ng