Gwamna El-Rufai ya bayyana matsayar Gwamnoni 36 a kan ‘Yan bindiga, ‘Yan ta'adda

Gwamna El-Rufai ya bayyana matsayar Gwamnoni 36 a kan ‘Yan bindiga, ‘Yan ta'adda

- Nasir El-Rufai ya ce babu wani rangwame ga ‘Yan bindiga da ‘Yan ta’adda

- Gwamnan ya ce gwamnoni sun cin ma matsayar a kashe duk wasu Miyagu

- Amma wani Gwamnan ya bayyana cewa wannan ba shi ne matsayarsu ba

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce duka gwamnonin jihohi sun hadu a kan bukatar hallaka ‘yan bindiga da duk wasu ‘yan ta’adda da ke jeji.

Daily Trust ta ce Malam Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen wani taro da aka shirya a Abuja, inda aka tattauna game da sha’anin karatun boko.

Gwamnan ya hakikance a kan cewa hanya daya da za a bi domin a samu kwanciyar hankali shi ne a kashe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da su ka fitini jama’a.

KU KARANTA: Zan bar Kaduna da zaran na kammala mulki - Gwamna

Da yake jawabi a ranar Talata a taron, gwamna na Kaduna ya ce duka gwamnoni sun amince a kan cewa jami’an tsaro su shiga cikin jeji su kashe miyagu.

Ya ce: “Dole jami’an tsaro su shiga kungurmin jeji, su kashe duka ‘yan bindiga. A kashe su duka.”

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce akwai bukatar a tarwatsa dajin da miyagu su ke fake wa, El-Rufai ya ce babu wani mai gaskiya da zai shiga jeji, ya na rayuwa.

A jawabinsa, Malam El-Rufai ya yabi kokarin shugaban hafsun sojojin sama da kokarin da yake yi na yi wa miyagun ‘yan bindigan da ke cikin jeji barin wuta.

KU KARANTA: Idris Deby ya shiga tsakiyar inda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ke a Sambisa

Har ila yau, gwamnan na jihar Kaduna ya sake tabbatar da cewa ba zai biya kudin fansa ba ko da kuwa masu garkuwa da mutane sun sace ‘dan da ya haifa.

Wani gwamna ya koka a kan yadda abokin aikinsa ya ke fito wa fili ya na fadan irin wadannan kalamai, ya ce ra’ayin El-Rufai dabam da matsayar gwamnoni.

Kwanaki aka ji matar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta na kuka akan yadda gashin dake kan mijinta ya yi furfura cikin kankanin lokaci a kan mulki.

Hadiza El-Rufai ta wallafa wani hotonsu, wanda su ka dauka ita da mijinta, ta ce wahalar mulki ya kara tsofar da dattijon maigidanta mai shekara 60 a Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng