Dattijuwa ‘Yar shekara 116 da aka yi shugabannin kasa 20 a idonta a Amurka ta rasu

Dattijuwa ‘Yar shekara 116 da aka yi shugabannin kasa 20 a idonta a Amurka ta rasu

- Hester Ford ta mutu bayan ta yi shekara 116 ta na shan miya a Duniya

- Kafin ta rasu, Hester Ford ce mutumiyar da ta fi kowa tsufa a Amurka

- Marigayiyar ta zo Duniya tun lokacin Roosevelt ya na Shugaban kasa

NBC ta rahoto cewa Hester Ford, mutumiyar Charlotte, a jihar North Carolina, ta rasu a gidanta a ranar Asabar, 17 ga watan Afrilu, 2021.

Wata tattaba-kunnen wannan Baiwar Allah, Tanisha Patterson-Powe, ta tabbatar wa WCNC cewa su na makokin mutuwar Miss Hester Ford.

Patterson-Powe ta fada wa ‘yan jarida: “Ko da cewa mu na bakin cikin abin da ya faru, amma mu na alfahari da sunan da ta bari a bayanta.”

KU KARANTA: Labarin rayuwar tsohon Shugaban kasar Chad, Marigayi Idris Deby

Ford ta mutu ta bar ‘ya ‘ya 12, jikoki 48, tattaba-kunne 108 da kuma kimamin jikokin jikoki 120.

Ana kyautata zaton an haifi marigayiyar ne a karshen 1905. Ana kwakwanto wannan Baiwar Allah ta kai shekara 116 ko akalla 115 a Duniya.

‘Yanuwan dattijuwar su ka ce Ford ta kasance jigo a dangi, ta na kaunar kowa, sannan ta kasance ta na ba duk tsatsonta gudumuwa a rayuwa.

“Ta zarce fiye da karni daya a Duniya, ta san abubuwan da su ka faru na fiye da shekaru 100.” ‘Yanuwanta su ka bayyana haka a Facebook.

Dattijuwa ‘Yar shekara 116 da aka yi shugabannin kasa 20 a idonta a Amurka ta rasu
Hester Ford Hoto: www.marca.com/en
Asali: UGC

KU KARANTA: Shiriya ta zo wa ‘Yan bindiga, sun zama Malamai masu wa’azi

A 1953 ta bar South Carolina, ta tafi Charlotte. A Nuwamban 2019 ne marigayiyar ta zama wanda ta fi tsufa a Amurka bayan rasuwar Alelia Murphy.

An haifi Hester Ford ne a garin Lancaster a South Carolina. A lokacin da Ford ta zo Duniya, Theodore Roosevelt ne shugaban kasar Amurka.

Kamar yadda lissafinmu ya nuna, kafin Ford ta bar Duniya, sai da aka yi shugabannin kasa har 20 a Amurka.

Kwanakin baya an ji cewa shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya yi tuntube har sau uku kuma ya fadi kan matakalan jirgin fadar shugaban kasa.

Wannan abin da ya faru ya haifar da alamar tambaya game da lafiyarsa. Biden mai shekara 78 shi ne shugaban kasar da ya fi tsufa a tarihin Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel