Jami’an Kwastam su na ajiyewa Najeriya Naira Miliyan 500 a duk ranar Duniya a shekarar 2021
- Jami’an hukumar kwastam sun tara kusan rabin Tiriliyan a shekarar nan
- Joseph Attah ya fitar da alkaluman nasarorin da su ka samu a farkon 2021
- Kwastam ta kuma yi ram da kayan Naira biliyan 2 da aka nemi shigo da su
The Cable ta rahoto Hukumar kwastam na kasa ta na cewa ta samu Naira biliyan 466 a matsayin kudin shiga a farkon shekarar nan da ake ciki ta 2021.
Babban jami’in da ke da alhakin hulda da jama’a na gidan kwastam, Joseph Attah, ya bayyana cewa sun samu wadannan makudan kudi a Q1 2021.
Alkaluman da aka fitar ya nuna jami’an kwastam sun samu kudin shigan da ya fi kowane yawa ne cikin watan Maris, inda aka tara Naira biliyan 169.4.
KU KARANTA: Rashin ma'aikata: Majalisa ta na son ganin Shugaban Kwastam
Hukumar da ke yaki da fasa-kauri ta samu Naira biliyan 157.6 a watan Junairu, sannan ta tara Naira biliyan 138.9 a watan Fubrairu mai karancin kwanaki.
A wata ukun farkon shekarar nan, hukumar ta tatso wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 216.9 a matsayin kudin da ake karba wajen shigo da kayayyaki.
Bayan haka kuma kwastam ta samu Naira biliyan 105.2 daga harajin VAT na kayayyakin masarufi.
Haka zalika, Joseph Attah ya bayyana cewa sun samu sauran kudin shigar ne daga kason da ake lafta wa masu shigo da kaya da kuma la’adar asusun tarayya.
KU KARANTA: Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka nemi a ketaro da su
Tsakanin watan Junairu zuwa Maris, hukumar ta karbe haramtattun kayan da darajarsu ta kai N1, 996, 145, 258.
Attah ya ke cewa a cikin wannan lokaci, hukumar kwastam ta karbe buhuna 37, 206 na shinkafa. A 2019 ne Gwamnatin tarayya ta haramta shigo da shinkafa.
Ana sa ran cewa kwastam za ta samu Naira tiriliyan 1.679 a shekarar nan. Idan aka cigaba da tafiya haka, hukumar za ta samu abin da ya zarce burin da ta ci.
Kwanakin baya ne majalisar wakilan tarayya ta bukaci a kara yawan kudin da hukumar kwastam ta ke harin za ta samu a bana daga N1.4tr zuwa N1.6tr.
Idan aka yi lissafi abin da jami’an kwastam su ke samu a duk rana ya kai akalla Naira miliyan 510.
Asali: Legit.ng