Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna

- An yi baran-baran a zaben yankin Arewa maso yamma na shugabannin PDP

- An shirya zaben bana ne a jihar Kaduna yau Asabar

- Wannan ya biyo bayan musayar kalamai tsakanin manyan jigogin jam'iyyar biyu

Rikici ya barke yayin zaben shugabannin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP na shiyar Arewa maso yammacin Najeriya ranar Asabar.

Wasu mambobin jam'iyyar sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda akayi tsarin zaben kuma hakan ya sa suka fasa akwatunan zaben kuma suka rikirkita wajen da ake zaben.

An gudanar da taron zaben ne a unguwar Rigachikun ta jihar Kaduna.

Ana cikin hotunan taron, ana iya ganin yadda aka fasa akwatunan zabe kuma aka rikirkita kujeru.

Wasu rahotannin sun nuna cewa an yi musayar kalamai kuma an baiwa hammata iska wanda hakan ya tilasta kawo karshen taron zaben.

Manyan masu takaran kujeran mataimakin shugaba na yankin Arewa maso yamma sune Sanata Bello Hayatudeen Gwarzo, Aminu Wali, da kuma wani na hannun daman tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

KU KARANTA: Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna
Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna Hoto Daga: BBC Hausa
Asali: Facebook

KU DUBA: An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna
Yanzu-yanzu: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna Hoto Daga: BBC Hausa
Asali: Facebook

Wannan rikici bai zo da mamaki ba, mun kawo muku cewa ga dukkan alamu, sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen arewa maso yamma, yayinda Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar Kano.

Kwankwaso wanda ya kasance daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu yayan jam'iyyar na Kano da ke adawa da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng