Da duminsa: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC

Da duminsa: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC

- Kyari ya ce akwai isasshen man fetur a dukkan gidajen man Najeriya kimanin Lita bilyan 2

- GMD na NNPC ya yi kira ga yan Najeriya kada su tada hankalinsu

Shugaban kamfanin man feturin Najeriya, Mele Idris Kyari, ya bayyana cewa ba zasu kara farashin Litan man fetur a watan Mayun nan ba.

Kyari ya bayyana hakan ne a zaman sulhun da ya jagoranta tsakanin mambobin kungiyar mammalakan motoci wato NARTO da kuma na kungiyar direbobin tanka PTD.

Za ku tuna cewa kungiyar direbobin tanka ta alanta shirin kaddamar da yajin aiki kan rashin fahimtar da ke tsakaninsu da mammalakan motoci.

Bayan zaman sulhun, direbobin sun dakatad da yajin aiki har sai bayan tattaunawa dake gudana tsakanin bangarorin biyu.

A cewar jawabin da hukumar ta saki ranar Litinin a shafinta na Facebook, Mele Kyari yace kasa ba zata kara farashin litan mai a watan Mayu 2021 ba.

DUBA NAN:Matsalar tsaro da Rashin hanyoyi masu kyau: Ahmed Musa ba zai buga wasannin 'Away' ba, Kano Pillars

Da duminsa: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC
Da duminsa: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC Credir: Nigerian National Petroleum Corporation
Asali: Facebook

KU KARANTA: An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta baci a Chadi

A bangare guda, kamfanin man fetur na NNPC ya bayyana cewa ya kashe kuɗi kimanin 53.36 biliyan wajen gyaran bututun man fetur a cikin watanni 11.

A cewar kamfanin masu satar man fetur a ƙasar nan na cigaba da ɓannata bututun man fetur ɗin wanda hakan ke saka NNPC cikin wani yanayi mara daɗi.

A rahoton da kamfanin ya fitar na wata-wata yace, haɗin guiwar da suka yi da mutanen wasu yankuna da kuma masu ruwa da tsaki ya fara haifar da ɗa mai ido, domin anfara samun sauƙin fasa bututun man fetur ɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel