Kwanaki tara bamu samu wanda ya mutu sakamakon COVID-19 ba, inji hukumar NCDC

Kwanaki tara bamu samu wanda ya mutu sakamakon COVID-19 ba, inji hukumar NCDC

- A karon farko tun bayan ɓarkewar cutar COVID19 a Najeriya, NCDC bata samu rahoton mutuwa daga cutar ba na tsawon kwanaki tara

- Hukumar ta bayyana hakane a rahoton da take fitarwa kullun, tace rabon da wani ya rasa ransa saboda cutar tun 11 ga watan Afrilu

- Sai-dai duk da wannan nasara, hukumar ta cigaba da yin kira ga yan Najeriya da kada su gajiya, su cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar musamman yayin da zasu yi tafiya

Hukumar dake kula da yaɗuwar cututtuka NCDC tace bata samu ko mutum ɗaya da ya mutu da cutar COVID19 ba na tsawon kwanaki tara a jere.

KARANTA ANAN: Sheikh Pantami ya bayyana wata babbar Nasarar da gwamnatin tarayya ta samu a ɓangaren Fasahar Zamani

NCDC tace ya zuwa yanzun mutane 2,061 ne suka rage waɗanda suke ɗauke da cutar a faɗin ƙasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ba'a sake samun wanda cutar ta kashe ba tun 11 ga watan Afrilu.

A rahoton da hukumar ta fitar tun kafin 11 ga watan Afrilu, adadin mutanen da suka mutu a mako na 14 cikin wannan shekarar shine mutum biyu daga jihohi biyu.

NCDC tace ta gudanar da gwajin cutar kimanin 1,870,915 tun daga 27 ga watan Fabrairu, 2020. Ta ƙara da cewa an sami mutane 120 da suka harbu da cutar a ranar Talata, wanda hakan yasa jimullar waɗanda suka taɓa kamuwa yakai 164,423.

Kwanaki tara bamu samu wanda ya mutu sabida COVID19 ba, inji hukumar NCDC
Kwanaki tara bamu samu wanda ya mutu sabida COVID19 ba, inji hukumar NCDC Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

Hukumar tace an sami ƙarin waɗanda suka harbu da cutar a ranar Talata daga jihohi bakwai. Wannan na kunshe ne a rahoton da hukumar ta fitar a shafinta na tuwita.

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Hakanan kuma NCDC ta bayyana cewa mutane 22 sun warke daga cutar cikin awanni 24 da suka gabata. Hakan yasa adadin waɗanda suka warke tun daga 27 ga watan Fabrairu, 22020 yakai 154,406.

Hukumar tace zata cigaba da yin duk me yuwuwa tare da jami'an lafiya don tabbatar da kare yan Najeriya daga kamuwa da cutar, kamar yadda tayi tun bayan ɓarkewar cutar zuwa yanzun.

Har ila yau, NCDC ta ƙara roƙon yan Najeriya da su cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar, waɗanda suka haɗa harda dokokin tafiye-tafiye.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci.

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'

Asali: Legit.ng

Online view pixel