Tsofaffin masu garkuwa da mutanen da su ka tuba, sun zama Fastoci a kudancin Najeriya

Tsofaffin masu garkuwa da mutanen da su ka tuba, sun zama Fastoci a kudancin Najeriya

- Cocin OPM ta dauki nauyin dawo da wasu tubabbun ‘Yan bindiga kan hanya

- Apostle Chibuzor Chinyere ya yi masu wa’azi, har an samu Fastoci a cikinsu

- Omega Power Ministries ta dauki nauyin iyalinsu, kuma ta koya masu sana’a

Wasu tubabbun ‘yan bindiga akalla takwas da su ka tuba, sun zama malaman coci a yanzu, inda su ke wa’adi a karkashin Omega Power Ministries.

Apostle Chibuzor Chinyere ya bayyana cewa tsofaffin tsageran Neja-Delta da masu garkuwa da mutanen da su ka yi horo, sun zama mutanen kwarai.

Jaridar Daily Trust ta ce Chibuzor Chinyere ya shaida wa hukumar dillancin labarai na kasa wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi jiya daga Abuja.

KU KARANTA: Kungiyar Kiristoci ta fito ta kare Ministan sadarwa, Isa Pantami

Babban limamin na cocin Omega Power Ministries, ya ce mutanen da aka sani a da a matsayin tsagera da masu garkuwa da mutane, sun tuba a yanzu.

Chinyere ya ke cewa shiriya ta zo wa wadannan tsofaffin ‘yan bindiga ne bayan an tirke su a dakunan bautan OPM, an yi masu wa’azin kiristanci.

“Na yi masu wa’azi, kuma wasu da yawa daga cikinsu, sun karbi wannan kira na wa, su ka mika rayuwarsu ga Yesu Almasihu.” Inji Chibuzor Chinyere.

Ya ce: “Kafin a kai ga daukar wannan mataki, sai da na saye wasu gidaje, na tattara su zuwa can.”

KU KARANTA: Hukuncin gwauron da ya na waya da Budurwarsa, ya yi maziyyi

Tsofaffin masu garkuwa da mutanen da su ka tuba, sun zama Fastoci a kudancin Najeriya
Hoton wani coci
Asali: UGC

Babban limamin cocin ya ce: “Lokacin da na fara yi masu wa’azi da farko, tun da su na cikin mutanensu, koma wa laifin da su ka baro, bai yi masu wuya ba”

“Saboda haka na yanke hukunci abin da ya fi dace wa shi ne su na bukatar sauyin wuri, wannan ne ya zama matakin farko da aka dauka na shiryar da su.”

Bayan karantar da su da aka yi, sai wasu takwas su ka zabi su zama malamai, wasu kuma su na aikin hannu. Bayan haka coci ta dauki nauyin iyalan mutanen.

Kwanakin baya kun ji labarin 'yan bindiga sun bi Sarkin Oye, Oba Obadu Oyewumi har gida sun dauke shi, amma ‘Yan Sanda sun ce su na yin bakin kokarinsu.

Wadannan miyagun 'yan bindiga sun bukaci a biya miliyoyi kafin su fito da Basaraken da su ka sace. 'Yanuwansa sun ce an lafta masu kudin fansa, miliyan 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel