Mai dakin El-Rufai ta zakulo kura-kurai 37 a sanarwar da PDP ta fitar a kan Kwankwaso

Mai dakin El-Rufai ta zakulo kura-kurai 37 a sanarwar da PDP ta fitar a kan Kwankwaso

- Jam’iyyar PDP ta fitar da sanarwar dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso

- Hadiza El-Rufai ta nuna akwai 'yan gyare-gyare a takardar da PDP ta fitar

- Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna ta fito da kura-kuran nahawu har 37

Hajiya Hadiza El-Rufai-Isma ta fito da tulin kura-kurai da jam’iyyar PDP ta tafka a takardar sanarwar dakatar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A jiya Hadiza El-Rufai-Isma ta yi wa takardar sanarwar da ‘yan tawaren jam’iyyar PDP na reshen jihar Kano su ka fitar a ranar 16 ga watan Afrilu, 2021.

Da farko mai dakin gwamnan jihar Kaduna ta ci gyaran amfani da babban baki da aka yi a jimlar farko a takardar da H. A Tsanyawa ya fitar ranar Juma’a.

KU KARANTA: Ba na cikin gwamnatin El-Rufai - Hadiza El-Rufai

Bayan haka, kwararriyar malamar harshen turancin ta ce akwai inda ya kamata ayi amfani da jami’i, amma aka bayyana kalmar korafi a matsayin tilo.

Kamar yadda aka gani a shafinta na Twitter, akwai inda Hadiza El-Rufai ta soki bangaren jimlar da aka rubuta kaco-kam, ta ce sakataren ya tafka kuskure.

Uwargidar gwamnan ta jihar Kaduna ta yi suka ne a matsayinta na wanda ta kware a kan harshen Ingilishi, babu ruwan ta da sha’anin siyasar Najeriya.

Akwai wurare kusan 30 da aka yi kuskuren amfani da bakaken kalmomi a inda ba su dace ba a sanarwar.

KU KARANTA: Ina tare da PDP, ba zan karbi tayin aikin Buhari ba - Hon. Ciroma

Mai dakin El-Rufai ta zakulo kura-kurai 37 a sanarwar da PDP ta fitar a kan Kwankwaso
Gyaran da Hadiza El-Rufai ta ci PDP
Asali: Twitter

Wannan takardar da bangaren na jam’iyyar PDP su ka fitar mai tsawon shafi daya ta gamu da cin gyara akalla 37 kamar yadda biron matar gwamnan ya nuna.

Kamar dai yadda aka santa, El-Rufai ce wanda ta kafa makarantar #KadunaLanguageClass a dandalin sada zumunta na Twitter domin inganta koyon harsuna.

Hajiya El-Rufai mai shekara 60 ta rubuta littafin ‘An Abundance of Scorpions’ da ya yi suna, sannan ita ce ta kafa gidauniyar @YELFFoundation da ke Kaduna.

Dazu kun ji cewa uwar Jam’iyya ta yi raddi a kan sallamar Rabiu Kwankwaso daga PDP, ta ce har yanzu tsohon gwamnan na Kano , Kwankwaso cikakken ‘Dan jam’iyya ne.

PDP ta ce babu wasu ‘yan halal da su ka dakatar da tsofaffin gwamnonin Kano da Neja daga jam’iyyar PDP kamar yadda ake yada wa a kafafen yada labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng