Ana tsakar azumi, Gwamnati ta soma biyan wasu daga cikin mutane 774, 000 da aka dauka aiki

Ana tsakar azumi, Gwamnati ta soma biyan wasu daga cikin mutane 774, 000 da aka dauka aiki

- Gwamnatin Tarayya ta soma biyan albashin wasu da aka dauka aikin SPW

- Festus Keyamo ya tabbatar da cewa NDE ta fara sakin kudin wasu ma’aikata

- Kwanakin baya ne aka dauki mutane 100 aiki cikin kowace karamar hukuma

Gwamnatin tarayya ta fara biyan N20, 000 a matsayin albashin ma’aikata 774, 000 da aka dauka aiki a karkashin tsarin ayyukan al’umma na musamman.

Karamin ministan ayyuka na kasa, Festus Keyamo (SAN), ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi da yamma, a shafinsa na Twitter.

Kafin yanzu, mutanen da aka dauka wannan aiki sun koka cewa an ki biyansu kudinsu a dalilin matsalar da aka samu wajen rajistar BVN dinsu a bankuna.

KU KARANTA: Daukar aiki: Buhari ne kadai zai ce mani kaza - Keyamo

Da yake bayani a Twitter, Festus Keyamo (SAN) ya ce daya daga cikin manyan bankunan da aka zaba ya biya ma’aikatan ya karkare aikin tantance BVN.

Festus Keyamo ya yi wa jawabin sa take da NDE commences partial payment of SPW stipends.Ma’ana an soma biyan wasu albashin wannan aiki.

Kayemo ya ce bayan ma’aikatar tattalin arziki ta fitar da kudi, ya bukaci ayi binciken kwa-kwaf kafin a soma biyan ma’aikan albashinsu a bankunansu.

A cewarsa, binciken ya zama dole ne bayan an gano ana samun shan ban-bam tsakanin sunayen asusun da ma’aikata su ka bada da bayanan da ke BVN.

KU KARANTA: An bayyana lokacin da za a fara daukar mutane 774,000 aiki

Keyamo: Gwamnati ta soma biyan wasu daga cikin mutane 774, 000 da mu ka dauka aiki
Ministan kwadago da samar da aikin yi, Festus Keyamo
Asali: UGC

Ministan ya ce bayan an kammala wannan bincike ne ma’aikatar samar da ayyuka ta kasa watau NDE, ta shiga biyan albashi ga wadanda aka tantance su.

Karamin Ministan kwadagon ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na jiran wasu bankuna bakwai ne su karkare aikin tantance BVN din ma’aikatan.

A karshe Keyamo ya tabbatar da cewa da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke yi na kawo wa jama’ar kasa sauki, ba tare da an bude kofar cin bulus ba.

Kwanaki kun ji gwamnatin jihar Ribas ta yi barazanar fita daga shirin daukar matasan da gwamnatin tarayya za ta ba ayyuka na masu karamin karfi.

Mai taimakawa gwamnan Ribas Nyesom Wike a kan sha’anin NDDC, Erastus Awortu, ya bada wannan sanarwa, inda ya koka cewa APC sun karbe aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel