An yi ram da wani wanda yake kawowa Mayakan Boko Haram asirin Sojoji inji DHQ

An yi ram da wani wanda yake kawowa Mayakan Boko Haram asirin Sojoji inji DHQ

- Sojoji sun yi nasarar kama wani da ake zargin ya na tona masu asiri

- Modu Ari ya na bin sahun Sojoji, sai ya sanar da Mayakan Boko Haram

- Irin wannan mugun aikin ya sa aka kai wa Rundunar soji hari a Yobe

Sojojin Najeriya sun ce dakarun Operation Lafiya Dole sun yi ram da wani da ake zargin ‘dan Boko Haram ne da yake yi masu leken asiri.

Kamar yadda gidan sojan ya bayyana, wannan mutumi ya na tattara sirrin dakarun Najeriya, ya je ya fa fada wa mayakan kungiyar Boko Haram.

Ana zargin cewa wannan mutumi ne ya yi sanadiyyar wani mummunan harin da ‘yan ta’addan su ka kai wa sojoji a yankin Kamuya, jihar Yobe.

KU KARANTA: Jami'an 'Yan sanda sun hallaka wasu 'yan bindiga a jihar Neja

Sanarwar da aka fitar ya ce darektan yada labaran sojojin kasa, Birgediya Janar Mohammed M. Yerima ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Da yake magana a jiya ranar Lahadi, 18 ga watan Afrilu, 2021, Janar Mohammed M. Yerima ya bada sunan wannan mutumi a matsayin Modu Ari.

Mai magana da yawun sojojin ya ce Modu Ari ya fada hannun dakarun 27 Task Force Brigade, inda ya amsa cewa ya na bibiyar sojojin Najeriya.

Ari ya na bin sahun sojoji, daga nan kuma sai ya kai wa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram labari.

KU KARANTA: ‘Dan Malam Jafar ya yi magana a kan mahaifinsa da rayuwa babu uba

An yi ram da wani wanda yake kawowa Mayakan Boko Haram asirin Sojoji inji DHQ
Shugaban hafsujn sojojin kasa, Janar I. Attahiru
Asali: Facebook

Kama wannan mutumi da aka yi ya sa rundunar sojojin kasar ta shiga bin diddiki domin cafke duk wadanda su ke yi wa ‘Yan Boko Haram leken asiri.

Jami’in ya ce: Ana bincike domin bankado sauran mutanen gari da ake hada baki da su ana samun sirrin sojoji, wanda hakan ke jefa jami’ai a cikin hadari.”

A cewar darektan yada labaran, leken asirin da ake yi wa sojoji a bangaren Timbuktu, ya jawo cikas.

A jiya aka ji cewa Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) da manyan hafsoshin tsaro sun kai ziyara zuwa garin Maiduguri, jihar Borno.

Ministan ya samu rakiyar Janar Lucky Irabor tare da sauran hafsoshin sojoji na kasa, inda su ka duba yanayin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel