Yanzu yanzu nan: Uwar Jam’iyya ta yi raddi a kan sallamar Kwankwaso daga PDP

Yanzu yanzu nan: Uwar Jam’iyya ta yi raddi a kan sallamar Kwankwaso daga PDP

- ‘Yan taware sun dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso daga PDP a jihar Kano

- Uwar jam’iyya ta ce tsohon Gwamnan jihar Kano ya na nan a PDP har gobe

- Haka zalika PDP ta karyata rade-radin cewa an sallami Dr. Babangida Aliyu

A ranar Lahadi, 18 ga watan Afrilu, ‘tan taware a jam’iyyar PDP ta reshen jihar Kano su ka dakatar da tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan mataki da bangaren Aminu Wali su ka dauka ya zo ne bayan rikicin da ya barke wajen zaben shugabannin jam’iyya na reshen Arewa maso yamma.

Ambasada Aminu Wali da ‘yan bangarensa sun zargi Rabiu Musa Kwankwaso da amfani da magoya-bayansa wajen tada rikici a zaben da aka shirya.

KU KARANTA: Abubuwan da za su kawowa manyan ‘Yan siyasan PDP cikas a 2023

A cewarsu, tsohon gwamnan na jihar Kano, Sanata Kwankwaso ya jawo wa jam’iyya abin kunya a dalilin amfani da ‘yan daba da ya yi wajen tarwatsa zabe.

Ba tare an saurari bangarensa, Sakataren ‘yan tawaren H. A. Tsanyawa, ya ce an dakatar da Rabiu Kwankwaso na tsawon watanni uku daga jam’iyyar ta PDP.

Jim kadan bayan fitowar takardar dakatar da jigon na PDP, sai uwar jam’iyya ta yi martani a jiya, ta ce har yanzuu Rabiu Musa Kwankwaso ya na nan a PDP.

PDP ta ce babu wasu ‘yan halal da su ka dakatar da tsofaffin gwamnonin Kano da Neja daga jam’iyyar PDP kamar yadda ake yada wa a kafafen yada labarai.

KU KARANTA: Za a mutu a 2023 - Kwankwaso

Yanzu yanzu nan: Uwar Jam’iyya ta yi raddi a kan sallamar Kwankwaso daga PDP
Manyan jam'iyyar PDP a taro
Asali: Twitter

Uwar jam’iyya ta fitar da jawabi ne ta bakin Kola Ologbondiyan, wanda ya ce akwai matakai da dokar PDP ta tsara wanda ake bi kafin a dakatar da mutum.

Kola Ologbondiyan ya gargadi masu yada wannan labari na karya da su guji wannan danyen aiki, ya ce PDP ba za ta yarda da abin da zai iya jawo hargitsi ba.

Ya ce: “PDP ta na tir da jita-jitar da ake yi da nufin kawo mana sabani, da jawo baraka a cikin mu.”

Kwanakin baya kun ji yadda rikici ya kunno kai a PDP a arewa maso yamma inda ake rigima tsakanin Rabiu Kwankwaso da Gwamna Aminu Tambuwal.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da gutsiri-tsoma da katsalandan a harkokin jam'iyyar PDP na reshen ihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel