A kai kasuwa: Tsohon ‘Dan Majalisar PDP da Shugaba Buhari ya ba mukami ya ce ba ya so
- Dr. Dayyabu Chiroma ya ki karbar mukamin da Gwamnatin Tarayya ta ba shi
- An zabi Chiroma a cikin majalisar da ke kula da babbar Makarantar Shendam
- Tsohon ‘Dan Majalisar ya aikawa Minista takarda, ya ce ba zai karbi aikin ba
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Bauchi, Honarabul Dayyabu Chiroma, ya ki karbar kujerar da gwamnatin tarayya ta ba shi.
Dr. Dayyabu Chiroma ya ki karbar ta yi da aka yi masa a matsayin ‘dan majalisar da ke sa ido a kan makarantar koyon aiki ta Shandam, jihar Filato.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, Dayyabu Chiroma, wanda ya wakilci Darazo a majalisar dokokin Bauchi ya ce ba zai ci amanar PDP ba.
KU KARANTA: PDP ta ruguza dakatarwar da ‘Yan taware su ka yi wa Sanata Kwankwaso
Chiroma ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aika wa babban Ministan ilmi na kasa, Mallam Adamu Adamu, inda ya bayyana dalilan karbar mukamin.
Tsohon ‘dan majalisar ya nuna jin dadi da aka ba shi wannan matsayi a gwamnatin tarayya, duk da cewa cikakken ‘dan jam’iyyar adawa ta PDP ne shi.
Amma duk da haka, Chiroma ya ce alakar da ke tsakaninsa da gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ba za ta bar shi ya karbi wannan mukami ba.
Haka zalika, Chiroma ya bayyana cewa ya na da kishin PDP, don haka ya zabi ya ki karbar wannan aiki.
KU KARANTA: Minista ya yi karin-haske, ya ce an fara biyan wadanda aka dauka aikin SPW
A wasikar ta sa, Chiroma ya yi matukar godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zakulo shi a cikin sauran mutanen Bauchi, ya ba shi wannan aiki.
“Dole in gode wa shugaban kasa da ya nuna ya yarda da ni in yi aiki a gwamnatinsa a wannan matsayi. Ina mai godiya da aka bani dama in yi wa kasa aiki.”
Yanzu haka, Dr. Chiroma shi ne shugaban hukumar yaki da safarar kwayoyi a Bauchi, kuma daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Kwanaki kun ji yadda rigima ta kaure tsakanin wasu ‘yan gida daya a wajen rabon gado, wannan rigima ya yi sanadiyyar da aka kashe babban yayan magadan.
Wadannan Bayin Allah sun hallaka yayansu domin su ci kudin da tsohonsu ya bari. Kawo yanzu an kama wasu daga cikin wadanda su ka yi wannan danyen aiki.
Asali: Legit.ng