Miji ya kone duk takardun kammala makarantun matarsa bayan fada ya hada su
- Ana iya samun fada tsakanin ma'aurata, amma yadda aka sarrafa zuciya yayin fadan nan shi ke nuna kaunar da ake ikirari
- Wata mai amfani da @Gwarimpagirl a Twitter ta wallafa yadda mijin abokiyar aikinta ya kona mata shaidar kammala karatunta
- Kamar yadda tace, tun daga shaidar kammala karatun firamare har zuwa na hidimar kasa ya kone mata saboda sun yi fada
Sannanen abu ne cewa ana samun sabani tsakanin ma'aurata, amma kuma iya sarrafa zukata yayin wannan sabanin shi ake kira da hankali.
Wasu ma'auratan kan rasa hankalinsu matukar fada ya hada su da juna, ta yadda suke yin abu tamkar tsoffin makiyan juna.
Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumunta ta Twitter tayi ikirarin yadda mijin wata abokiyar aikinta ya kone mata dukkan takardun shaidar kammala karatunta bayan fada ya hada su.
KU KARANTA: Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake
Mai amfani da Twitter mai suna @Gwarimpagirl ta wallafa: "Abokiyar aikina tayi fada da mijinta kuma ya dauke dukkan takardun shaidar kammala karatunta ya kone su.!"
Ta kara da bayyana cewa, mijin ya kone takardun matarsa tun daga na shaidar kammala karatun firamare zuwa shaidar hidimar kasarta.
Ta rubuta, "Asalin takardun, tun daga firamare har zuwa shaidar hidimar kasarta."
Ga wasu daga cikin martanin da aka yi mata:
Wani mai amfani da suna @unikmona cewa yayi: "Darasi! Ku gujewa duk wanda yake barin zuciya ta rinjayesa. Zasu iya soka maka wuka a wannan lokacin kuma daga baya su yi taushi."
@whiteman kuwa cewa yayi: "Hassada ce na hango. Ta maka shi a kotu. Wanne irin rashin hankali ne wannan? Sai dai kuma idan shi ya biya mata kudin makarantan, duka da hakan bai bashi wannan lasisin ba."
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi kuma shugaban kwamitin tuntuba na jam'iyya mai mulki ta APC, Yahaya Bello, ya ce gwamnoni masu yawa daga jam'iyyar PDP da sauran manyan jam'iyyu na kokarin komawa APC.
Wannan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi na cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya tsaf domin barin jam'iyyar PDP zuwa APC.
Yayin zantawa da manema labarai bayan taron sirri da yayi da kwamitinsa a hedkwatar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a Abuja, Gwamna Bello yace jam'iyyar adawa ta san abubuwan dake faruwa a APC.
Asali: Legit.ng