Neman Duniya ta sa sun kashe ‘Danuwansu saboda su lakume gadon Mahaifinsu da ya rasu

Neman Duniya ta sa sun kashe ‘Danuwansu saboda su lakume gadon Mahaifinsu da ya rasu

- ‘Yanuwa sun hada-kai sun hallaka ‘Danuwansa saboda sabanin rabon gado a Imo

- Wani ‘danuwan mamacin ya rankwala masa karfe, hakan ya yi sanadin cikawarsa

- Ko da aka gaggauta aka kai Bawan Allah zuwa asibiti a Okuku, sai aka ji ya rasu

A ranar Talata wata musiba ta auku a Okuku, garin Owerri da ke jihar Imo inda wasu ‘yan gida daya su ka bugi babban yayansu, har ya bar Duniya.

Punch ta fitar da rahoto cewa ‘yanuwan jini sun kashe Chinonso Azuatalam ne a dalilin sabanin da su ka samu wajen raba dukiyar mahaifinsu da ya mutu.

Chinonso Azuatalam wanda aka fi sani da Dakwada ya mutu ya bar iyalinsa da ciki a sakamakon mummunan bugun da ‘yanuwansa su ka yi masa.

KU KARANTA: Na-kusa da Sheikh Jafar Adam ba su yi watsi da mu ba - ‘Dan sa

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa marigayin duka ne a gaban ‘yanuwan mahaifiyarsa wadanda su ka zo su karbi gadon da ake rikici a kansa.

Wata majiya ta ce marigayin ya na fada da kaninsa mai suna Chibuzor, sai ‘danuwan na sa na jini ya rankwala masa wani karfe a keya, nan-take ya kife.

An garzaya da Chinonso zuwa wani asibiti, inda ana isa aka tabbatar cewa ba ya numfashi.

Bayan ‘yanuwan mamacin sun samu labarin ya cika, sai su kayi maza, su ka tsere. Chibuzor wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘danuwansa, tagwaye ne.

KU KARANTA: An ba Shugaban PCACC cin hanci domin a rufe binciken Masarautar Kano

Neman Duniya ta sa sun kashe ‘Danuwansu saboda su lakume gadon Mahaifinsu da ya rasu
Shugaban 'Yan Sanda na kasa, Usman Alkali Baba
Asali: Twitter

Bayan nan, wata ‘yaruwar marigayin, Chioma Azuatalam, wanda jami’ar ‘yan sanda ce ta yi wa mai dakin Chinonso mai dauke da juna biyu mugun duka.

Shugaban mutanen kauyen Okuku, Martin Daniel, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce an kama ‘yaruwar mamacin da ta yi wa matarsa dukan.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Imo, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da cewa Chioma da daya daga cikin ‘danuwan mamacin sun shiga hannunsu.

A yau ne ku ka ji cewa shugaban kasar Faransa, Emmauel Macron ya yabi shugaban kamfanin BUA a kan kafa wata babbar matatar mai a Kudancin Najeriya.

Bayan wannan jinjina, kasar Faransa ta karrama, Abdul Samad Rabiu, sannan ta gayyaci shugaban kamfanin na BUA zuwa wani taro da za ayi a Faris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel