Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo

Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo

- Kungiyar Ohanaeze ta bayyana cewa yan kabilar Igbo na samu kwanciyar hankali a Arewa

- Wannan ya biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi na ballewar Igbo daga Najeriya

- Hakazalika an fara kaiwa yan Arewa mazauna kasar Igbo hari

Kungiyar kare hakkin yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta siffanta Arewacin Najeriya a matsayin wurin da yan kabilarsa suka fi samun kwanciyar hankalin rayuwa da kasuwanci.

Shugaban kungiyar na shiyar jihohin Arewa 19, Augustine Amaechi, a ranar Juma'a a Abuja ya bayyana cewa Arewa ta baiwa Igbo masauki fiye da yadda ake tsammani.

Amaechi ya ce akan samu sabani wasu lokuta saboda a rayuwa dole a samu hakan.

KU DUBA: Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko

Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo
Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo
Asali: UGC

KU KARANTA: Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari

A kan maganar ballewar da Igbo ke yunkuri yi daga Najeriya, ya ce rashin ayyukan yi ya sabbaba hakan.

Ya kara da cewa tun da Igbo sun shahara da kasuwanci, suna bukatan Arewa domin tara arziki.

"Magabatanmu na cewa duk da cewa matasanmu sun fusata, muna bukatar garambawul a kasar nan ba ballewa ba saboda ba zaka iya sayar da kayarka a kauyenka ba," Yace.

Shi kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na kasa, George Obiozor, ya ce al'ummar Igbo ba su yaki da kowa.

"Abinda muke so kawai shine daidaito da sauran jama'a. Lokaci ya yi da zamu fadawa shugabanni gaskiya," yace.

A bangare guda, Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an sake kai hari kan yan Arewa mazauna jihar Imo inda aka hallaka akalla mutum bakwai.

A cewar rahoton, wannan sabon harin ya auku ne makon da ya gabata inda aka kashe mutum hudu a Orlu kuma mutum uku a garin Amaka.

Wani mazaunin Owerri, Dr. Lawan Yusuf, ya bayyana cewa yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ne suka kai harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel