Aikinka ya na kyau, Shugaban kasar Faransa, Macron ya fadawa Mai kamfanin BUA

Aikinka ya na kyau, Shugaban kasar Faransa, Macron ya fadawa Mai kamfanin BUA

- Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yabi kokarin Abdul Samad Rabiu

- Macron ya jinjinawa Abdul Samad Rabiu a kan matatar man da yake ginawa

- Kasar Faransa ta gayyaci shugaban kamfanin na BUA zuwa wani taro a Faris

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya jinjina wa shugaban kamfanin Abdul Samad Rabiu, a game da matatar da yake gina wa a Akwa Ibom

Ganin yadda aikin wannan matatar tace danyen mai yake tafiya, jaridar The Cable ta ce shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yaba wa aikin kamfanin.

Ministan kasuwancin kasar wajen Faransa, Franck Riester, ya bada sanarwar jinjinar shugaban kasar Faransa a lokacin da ya ziyarci Hedikwatar BUA a Legas.

KU KARANTA: Nan da wasu watanni, fetur zai kara kudi a kasuwanni da gidajen mai

Ministan ya kuma mika wa Abdul Samad Rabiu takardar gayyata inda ake bukatar ya halarci wani taro na harkar kasuwanci tsakanin Afrika da Faransa.

Za a yi wannan babban taro ne a watan Yuni mai zuwa a babban birnin kasar Faransa, Faris.

Har ila yau, Ministan Faransan ya bayyana Rabiu a matsayin shugaban France Nigeria Investment Club.

Ministan wanda ya yi magana da yawun shugaba Emmanuel Macro, ya ce Faransa a shirye ta ke ta bada gudumuwarta wajen ayyukan da za su taimaki jama’a.

KU KARANTA: BUA ya bada kyautar naira biliyan 1 don yaki da COVID-19

Aikinka ya na kyau, Shugaban kasar Faransa, Macron ya fadawa Mai kamfanin BUA
Abdul Samad Rabiu da Franck Riester Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ministan kasar wajen ya samu shaida hannun da aka sa tsakanin kamfanin BUA group da Axens domin tabbatar da yadda aikin gina matatar da ake yi yake tafiya.

An rahoto Franck Riester ya na cewa: “Ina farin cikin ganin yadda Abdul Samad Rabiu ya dage wajen kafa matatar danyen man nan domin taimaka wa al’umma."

A shekarar bara ne BUA ta sa hannu da kamfanin Axens na kasar Faransa a kan gina matatar da za ta rika tace ganguna 200, 000 na danyen mai a jihar Akwa Ibom.

wannan matata da za a gina za ta rika tace ton miliyan 10 na danyen mai a shekara, sannan kuma za ta rika samar da sinadarai kamarsu Euro-V fuels da Polypropylene.

Asali: Legit.ng

Online view pixel