Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu

Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu

- Tsohon gwamnan Legas ya nesanta kansa da rabon shinkafa da akayi a Legas

- A makon da ya gabata, an rabawa mutane kayan hatsi mai dauke da hotunan dan siyasan

- Tinubu ya ce duk da ba shi ya sa ayi ba, yana alfahari da hakan

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba da saninsa aka rabawa al'ummar jihohin arewa shinkafa dauke da hotunansa ba amma ya ji dadin hakan.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, a rattafa hannu kuma kamfanin dillancin labarai NAN ta samu, a Legas.

"Mun ga hotunan buhuhunan shinkafa dauke da hotunan Asiwaju da ake rabawa a jihohin Arewacin Najeriya," Tinubu yace.

"Ba ni na dauki nauyin wannan abu ba amma ina yabawa kungiyoyin masu goyon bayansa da suka yi wannan muhimmin sadaka musamman cikin watan Ramadan mai alfarma."

KU KARANTA: Bashin da ake bin Najeriya ya kai N33.63 Trillion, Ofishin manajin basussuka DMO

Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu
Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu
Asali: Instagram

KU DUBA: Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko

Yayinda ake gab da shiga watan Ramadana, an yi rabon buhuhunan shinkafa da kayan hatsi da hotunan tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a jihar Kano.

A hotuna da bidiyoyi da suka bazu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, an ga mutane da buhuhunan shinkafa mai rubutun ‘JAGABA - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu’ ana raba musu.

Wata mai suna @mansurah_isah a shafin Instagram ta daura hotunan inda take godiya ga gidauniyar Tinubu kan wannan kayan abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel