Jaruma mai kayanmata ta wallafa wasu bidiyo na taya ma'aikatanta 4 murnar aurensu

Jaruma mai kayanmata ta wallafa wasu bidiyo na taya ma'aikatanta 4 murnar aurensu

- Fitacciyar mai siyar da kayanmata, Jaruma Empire, ta yi wallafa inda ta sanar da cewa ma'aikatanta hudu sun yi aure

- Gagarumar 'yar kasuwar ta wallafa bidiyoyi inda biyu daga cikin matan ke nuna wasu irin tufafi na alfarma

- Jaruma ta yi kira ga mabiyanta da su nuna kauna ga matan ta hanyar taya su murnar wannan nasara

Fitacciya kuma gagarumar mai siyar da kayan mata, Jaruma, ta wallafa wani labari mai dadin ji dangane da wasu ma'aikatanta a shafinta na Instagram.

A wallafar wacce tayi a ranar Laraba, 14 ga watan Afirilu, ta sanar da cewa mata hudu cikin ma'aikatanta ne suka yi aure a wannan shekarar.

Jaruma ta wallafa bidiyo tare da matan biyu, a na farko tana gwada kalar jikinta da wasu tufafi tare da matan.

KU KARANTA: Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan abokinsa ya je huce gajiya

Jaruma mai kayanmata ta wallafa wasu bidiyo na taya ma'aikata 4 muran bayan sun yi aure
Jaruma mai kayanmata ta wallafa wasu bidiyo na taya ma'aikata 4 muran bayan sun yi aure. Hoto daga jaruma_empire
Asali: Instagram

KU KARANTA: Makomar Afrika: Wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya ta kwace kambun nahiyar

A bidiyon na biyu, fitacciyar 'yar kasuwan ta mika godiyarta ga matan biyu inda ta kira su da masoyanta bayan ta siya wani gashi na N375,000 amma mai gyaran kanta bata samu zuwa ta saka mata ba.

A bidiyo na uku, an ga jaruma sanye da kayan tamkar mai magani yayin da take sauraron korafin daya daga cikin matan.

A karkashin bidiyon, 'yar kasuwar ta rubuta: "Shekarar 2021 ta ma'aikatan Jaruma ce. Hudu daga cikinsu sun yi aure. Pikky, Hauwa, Chisom da Jane. Zan wallafa bidiyonsu daya bayan daya. Don Allah ku nuna musu kauna."

A wani labari na daban, wata mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Oluwatosin Adeniji, ta zargi Omoyele Sowore da neman tallafi da sunanta kuma ya samu ya adana.

A ranar Talata, 14 ga watan Afirilu ne ta je shafinta na Twitter inda tayi yayata ga Sowore akan yadda ya nemi tallafi da sunanta ba tare da ta sani ba.

Wani sashin wallafarta yace: "Sowore, abun takaici ne yadda kayi amfani da sunana tare da wahalar da na sha. Na je gidan yari a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kan EndSARS amma ka nemi tallafi da sunana ba tare da ka sanar dani ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel