S&P Global Platts: Farashin man fetur zai tashi sama a cikin tsakiyar shekarar 2021

S&P Global Platts: Farashin man fetur zai tashi sama a cikin tsakiyar shekarar 2021

- S&P Global Platts ta na hangen tashin farashin danyen mai a kasuwa

- Kamfanin ya ce mai zai kara tsada a tsakiyar shekarar nan da ake ciki

- Raguwar adadin man da ake hakowa a kullum zai sa farashi ya tashi

Kamfanin S&P Global Platts ya yi hasashen cewa farashin gangar mai a kasuwa zai zarce fam Dala $70 a tsakiyar shekarar nan ta 2021 da ake ciki.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa za a samu karin bukatar mai nan da ‘yan watanni zuwa Agusta.

Wannan kamfani na masu bincike da nazari ya bayyana cewa kasashen da su ke amfani da mai sosai irin Indiya za su jawo man da ake hako wa ya karu.

KU KARANTA: Buhari ya na kokarin ba Majalisa da Kotun jihohi damar cin gashin-kansu

Hakan ba zai yi wa kungiyar OPEC ta kasashen da ke hako danyen mai dadi ba domin ta na kokarin ganin an rage adadin hakon da ake yi a kowace rana.

Ko da akwai matsalolin da ake hange game da samuwar mai a ‘yan shekarun nan, an fi sa ido a kan yanayin da annobar COVID-19 ta jefa masu bukatar man.

A dalilin annobar COVID-19 da ta auka wa kasashen Duniya, darajar gangan mai ya yi kasa.

Rashin tsadar da man ya yi, ya jawo kamfanoni sun kara yawan abin da su ke hako wa a duk rana domin ganin sun tara riba mai yawa a cikin wannan lokaci.

KU KARANTA: Matar da ta takali Gwamnatin Kano a kan yaki da COVID-19 ta bani

S&P Global Platts: Farashin man fetur zai tashi sama a cikin tsakiyar shekarar 2021
Karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva
Asali: Twitter

S&P Global Platts ta ce nan da watan Satumban shekarar nan, zai zama cewa abin da kasashen OPEC su ke hako wa a duk rana bai kai ganga miliyan hudu ba.

Haka zalika S&P Global Platts ta na ganin cewa kasar Saudiya ce za ta dage da hako danyen man.

Idan adadin abin da ake haka ya ragu, za a yi fama da karancin mai a Duniya, wanda hakan zai zaburar da farashi ya tashi har ganga ta haura $70 nan da watanni.

A makon nan ku ka ji cewa 'yan ta’addan Boko Haram sun yi kaca-kaca da Garin Damasak, inda l’umma duk su ka tafi gudun hijira, su ka bar gawawwaki babu jana’iza.

Duk wanda zai iya ya bar Damasak bayan Boko Haram sun kai hari shida a mako biyu. Lamarin har ya kai 'yan ta'addan sun kafa tuta a karamar hukumar Mobbar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel