Masu yi da gaske: Abdul Samad Isyaka Rabiu ya bayar da kyautar naira biliyan 1 don yaki da COVID-19
A kokarinsa na hada kai domin ganin an ci galaba a kan annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Isiyaka Rabiu ya sanar da kyautar naira biliyan 1 ga gwamnatin tarayya.
Haka zalika, baya ga tallafin tsabar kudi N1,000,000,000 a yanzu haka Abdul Samad ya yi odan karin kayan asibiti da kuma hada da na’urori, injina da kayan gwajin cutar Coronavirus da za’a yi amfani dasu a jahohi guda 9.
KU KARANTA: Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sanya dokar hana shiga da fita a jahar
Maganan da ake a yanzu shi ne kayan nan na kan hanya, kuma za su sauka Najeriya nan bada jimawa, daga cikin jahohin da za su ci amfani wannan tallafi akwai Legas, Kano, Adamawa, Edo, Kwara, Rivers, Abia, Akwa-Ibom da Sokoto.
Da yake jawabi, Abdul Samad ya bayyana cewa akwai bukatar kamfanoni masu zaman kansu su tallafa ma gwamnati wajen kawar da cutar Coronavirus, sa’annan yace tallafin N1,000,000,000 da ya yi alkawari zai bayar ne ta hannun babban bankin Najeriya, CBN, a karkashin tsarin “Private Sector Coalition Committee against COVID-19”.
“Tallafin nan zai kara rage ma gwamnati adadin kudin da take bukata wajen kashe ma hukumar dake yaki da yaduwar cututtuka a kasa, NCDC, haka zalika zai zamo kariya ga jami’an kiwon lafiya dake yaki da cutar.
“Kowacce jaha za ta samu kyallen rufe fuska guda 100,000, kayan sawa a jiki na kariya ga jami’an kiwon lafiya guda 1000, gilasan kariya guda 2000, safar hannu 1000, kayan gwaji 1000 da sauran kayayyaki.” Inji shi.
A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Akwa Ibom ta dauki matakin kulle iyakokinta da makwabta jahohi tare da hana zirga zirgan ababen hawa daga shiga ko fita jahar har sai yadda hali ya yi sakamakon bullar cutar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.
Koda yake babu wani labarin bullar cutar a jahar, amma gwamnatin ta dauki matakin ne don kare yaduwarsa zuwa jahar, don haka ta umarci ma’aikata su koma zaman gida daga ranar 30 ga watan Maris.
Sakataren gwamnatin jahar, Emmanuel Ekwuem ne ya sanar da haka da safiyar Alhamis, 26 ga watan Maris, inda ya umarci jama’an jahar su yi zamansu a gida, sa’annan ya bayyana cewa gwamnati za ta hada hannu da Yansanda don tabbatar da dokar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng