Mun shiga uku: ‘Yan bindiga sun aukawa 2/3 na Jihohin Najeriya, su na ta'adi inji Gwamna

Mun shiga uku: ‘Yan bindiga sun aukawa 2/3 na Jihohin Najeriya, su na ta'adi inji Gwamna

- Gwamna Samuel Ortom ya yi ikirarin ‘Yan bindiga sun shiga Jihohi akalla 24

- Ortom ya ce rikicin ‘Yan bindigan zai iya haddasa matasalar karancin abinci

- Sanata Ali Ndume na ganin akwai laifin shugabanni wajen hura wutan rikicin

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya ce a halin yanzu ‘yan bindiga su na barna a jihohi akalla 24 da ake da su a Najeriya da kuma birnin tarayya.

Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma Samuel Ortom ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi magana a taron kungiyar ‘yan jarida (NUJ) na reshen garin Abuja.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, an gayyaci gwamnan a matsayin mai jawabi a taron kungiyar, inda Mohammed Ali Ndume ya shugabanci zaman da aka yi.

KU KARANTA: ‘Yan ta’adda sun yi kaca-kaca da Damasak, ana gudun hijira a Nijar

Da yake jawabi ta yanar gizo, Ortom ya ce idan ba a dauki mataki tun wuri ba, barnar da ‘yan bindiga su ke yi zai kai ga matsalar karancin abinci a Najeriya.

“Akalla johohi 26 cikin 36 na Najeriya su na fuskantar mummunar rigimar makiyaya da manoma, wanda hakan yake haddasa kashe-kashe” inji gwamna Ortom.

Ya ce: “Idan ba a samar da dokokin kiwo ba, makiyaya za su auka wa gidan kowa a kasar nan, kuma wannan barazana ne ga noman abinci a fadin kasar nan.”

Ortom ya bada shawara, “Za a kawo karshen rikicin makiyaya ne idan aka haramta kiwo a fili gaba daya.”

KU KARANTA: Rade-radin sauya-sheka: Gwamnan Zamfara ba zai iya shiga APC ba

‘Yan bindiga sun aukawa 2/3 na Jihohin Najeriya da Birnin Tarayya, su na barna – Gwamna Ortom
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce kasashen Duniya sun shigo da sabon tsarin kiwo ta yadda makiyaya ke killace dabbobinsu, ya ce har a Afrika an fara daukar wannan dabarar.

Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya zargi gwamna Samuel Ortom da jawo rikicin kabilanci a jiharsa ta Benuwai.

Sanata Ndume a na shi bangaren ya zargi gwamnoni da sauran shugabanni da hura wutar fitinar, ya ce shugabanni ba su komai illa hada-kan mutane, su yi ta fada.

Kafin yanzu kun samu labari cewa babban jigon APC, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi kwanaki cikin ragar hukumar EFCC, inda ake bincikensa.

Sanata Rochas Okorocha wanda ya sauka daga mulki a matsayin gwamnan jihar Imo a 2015, ya na fuskantar zargi na badakalar lakume wasu biliyoyi daga baitul mali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel