Dalilin Hukumar EFCC na cigaba da rike tsohon Gwamna Okorocha bayan kwana 2

Dalilin Hukumar EFCC na cigaba da rike tsohon Gwamna Okorocha bayan kwana 2

- Sanata Rochas Okorocha ya shafe kwanaki biyu ya na tsare a wajen EFCC

- Wata majiyar EFCC ta bayyana abin da ya sa tsohon Gwamnan yake tsare

- Ana bukatar Sanata Okorocha ya yi wasu bayanai kafin a iya bada belinsa

Sanata Rochas Okorocha ya na cigaba da shan zama a hannun jami’an hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Fiye da sa’o’i 24 bayan an kama tsohon gwamnan na jihar Imo, ya na cigaba da shan matsa a kan zargin aikata rashin gaskiya da tafka badakalar biliyoyi.

Jaridar The Nation ta ce har zuwa ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021, da kimanin karfe 5:00 na yamma, ba a fito da Sanata mai-ci, Rochas Okorocha ba.

KU KARANTA: EFCC ta kama Okrocha a Abuja, an yi gaba da shi

Wata majiya daga hukumar EFCC ta ce: “Ana yi wa tsohon gwamnan (na jihar Imo) tambayoyi a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Bai samu beli ba tukuna.”

Majiyar ta ce ana bukatar Sanatan na Imo ta yamma ya yi karin haske game da wasu kudi da su ka fita.

“Zuwa yanzu ya na ba jami’anmu hadin-kai. Ya na bukatar ya duba wasu takardu ne, sannan ya bayyana abin da ya faru ta bangarensa.” Inji wannan Jami’i.

Rahotannin Premium Times sun bayyana cewa EFCC sun cafke Okorocha ne bayan sun shafe kusan sa’o’i biyar ana gwabza wa da shi a gidansa a Abuja.

KU KARANTA: Okoracha ya yi takaddama da Sarki a jirgin sama

Dalilin Hukumar EFCC na cigaba da rike tsohon Gwamna Okorocha bayan kwana 2
Sanata Rochas Okorocha
Asali: Facebook

Bayan an yi masa tambayoyi a ranar farko, a karshe sai dai tsohon gwamnan ya kwana a ofishin hukumar EFCC da ke unguwar Wuse 2 a birnin tarayya Abuja.

Washegari aka cigaba daga inda aka tsaya, abin da hadiminsa, Sam Onwuemeodo, ya ce an yi ram da shi ne kan wani tsohon korafi daga wajen gwamnatin Imo.

Rochas Okorocha shi ne fitaccen ‘dan siyasa na farko da jami’an EFCC su ka cafke tun bayan zaman Abdulrasheed Bawa sabon shugaban hukumar kwanaki.

Kwanaki kun ji cewa an kama tsohon Gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, bayan ya kuskura ya sake bude otel din Royal Palm Estate da aka garkame.

Tsohon gwamnan ya taka kafa tare da rakiyar surukinsa, Uche Nwosu, inda ya doke sakatar da aka sa wa wannan otel da ake zargin mai dakinsa ce ta mallaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel