Sanusi vs Ganduje: An kaddamar da sabon bincike kan masarautar Kano

Sanusi vs Ganduje: An kaddamar da sabon bincike kan masarautar Kano

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, na fuskantar sabon bincike daga hukumar yaki da rashawar jihar kan zargin sayar da wasu dukiyoyin masarautar, Daily Trust ta tattaro.

Rahotanni sun bayyana cewa masarautar ta shiga yarjejeniyar kasuwanci da wata kamfani Capital Properties Nigeria Limited (CPNL), na gini a filin Gandun Sarki dake Hotoro, karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Masarautar ta nada kwamitin mutane shida karkashin jagorancin Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim, ne domin wanzar da yarjejeniyar da akayi da kamfanin CPNL.

A makon da ya gabata, hukumar yaki da rashawan ta damke mambobin kwamitin biyu kan zargin karban cin hancin milyan ashirin da sunan yan gaban sarki sarkin Kano kuma za'a gurfanar da su gaban kotu.

Yayinda aka tuntubi shugaban kwamitin, Jarman Kano, ya bayyana cewa masarautar Kano ce kadai za tay iya mgana kan lamarin. Har yanzu dai masarautar ba tayi tsokaci ba.

Wannan sabon binciken na zuwa ne yan kwanaki bayan nasarar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a kotun koli.

Gwamnan ya kasance cikin takun saka da Sarkin kuma wasu na ganin cewa wannan wani sabon shirin cigaba da rikicin dake tsakaninsu ne.

Sabanin Gandun Sarkin dake Hotoro, ana zargin masarautar Kano da sayar da wasu filaye a Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

Bayan haka, an yi zargin cewa an sayarwa kamfanin CPNL filin ne a kudi N70m.

Daga baya kuma aka ce an yanka filayen fuloti-fuloti kuma aka sayarwa mutane milyan daya-daya da kuma N360,000 ga kanana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel