Tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

– A rana irin ta yau aka kashe Malam Ja’afar Mahmud Adam

– Wasu suka kashe babban Malamin yana tsakiyar sallar asuba

– Sheikh Ja’afar yana cikin manyan Malaman da aka yi a Arewa

Tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
Hoton Marigayi Jafar Adam daga Jaridar Daily Trust

A dalilin tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Daura da aka kashe shekaru 10 da suka wuce Legit.ng tayi wannan rubutu. An dai kashe Malam Ja’afar yayin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin da yake Limanci.

Har yau dai ba a kama wadanda ke da hannu wajen kashe babban Malamin ba wanda ya ba addini rayuwar sa. An dai haifi Malam Ja’afar a Garin Daura a gidan Malamai, nan ya fara karatun addini daga nan ya koma Kasar Kano inda yayi almajiranci.

KU KARANTA: Shirin kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
A rana irin ta yau aka kashe Malam Ja’afar Mahmud Adam

Daga nan ya kara karatun addini da boko a Garin Kano har ya samu nasara a gasar karatun Al-kur’ani. Daga nan Malamin ya samu wucewa Kasar Saudiyya inda ya Digiri a fannin Ilmin Al-Kur’ani a Jami’ar Madina.

Bayan ya kammala kuma ya zarce Kasar Sudan inda ya samu Digiri na biyu a fannin yaren larabci. A lokacin da aka kashe Sheikh Jafar yana digirin sa na uku a fannin addini Musulunci a Jami’ar Danfodiyo ta Sokoto.

KU KARANTA: Ana iya samun wani rikici bayan Boko Haram

Marigayi Ja’afar yana cikin malaman da suka kware wajen tafsirin Al-kur’ani da kuma iya bayani dalla-dalla ga Jami’a bisa koyarwar Sunnah. Malam Jafar ya koyar da al'umma ilmi da dama na Tauhidi da Hadisi da Sira da Fikihu na tsawon lokaci a Kano, Kaduna, Bauchi, Maiduguri dsr.

Allah ya jikan Marigayi Malam Jafar. Ameen.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaki da Boko Haram a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel