Makomar Afrika: Wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya ta kwace kambun nahiyar

Makomar Afrika: Wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya ta kwace kambun nahiyar

A ranar Litinin ne Twitter ta sanar da bude hedkwatar ta a Ghana. A yayin amsa tambayar me yasa aka zabi Ghana, Twitter tace Ghana ce jarumar damokaradiyya domin tana goyon bayan fadin ra'ayi, wanda Twitter ke rajin karewa.

'Yan Najeriya sun dinga hayaniya a kafar sada zumunta ta Twitter inda suka dinga dorawa gwamnatin Najeriya laifin rashin tabbatar da dokoki da salon da zasu janyo masu saka hannayen jari. Akwai dan Najeriyan da yace Jack Dorsey ya kasa samun layin waya a Najeriya ne saboda miyagun dokokin rijista.

Amma kuma, matsalar ta fi abu daya kamar yadda wasu suke gani. Sannanen abu ne yadda a watannin nan Ghana ke doke Najeriya tare da karbe kambun gawurta na nahiyar Afrika.

Ga wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya.

KU KARANTA: Ku tuhumi magabatana a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya

Makomar Afrika: Wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya ta kwace kambun nahiyar
Makomar Afrika: Wurare 7 da Ghana ta doke Najeriya ta kwace kambun nahiyar. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Saka hannayen jari kai tsaye daga kasashen ketare

Najeriya ce kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar kamar yadda bankin duniya ya sanar. Ta ninka kasar Ghana sau bakwai a GDP.

A tsammanin mai karatu, Najeriya za ta fi jan hankalin masu saka hannayen jari, amma hakan ba gaskiya bane.

A 2020, NBS ta bayyana cewa Najeriya ta samu $414.79 miliyan na hannayen jari a cikin wata tara. Amma Ghana ta samu $785.62 miliyan a cikin wata shida, duk da karfin tattalin arzikin Najeriya.

Kamfanonin motoci sun koma Ghana

Masu hankali na cewa kasuwa ba yawan jama'a bace, yawan jama'ar da za su iya siyan kaya ne. Kusan rabin 'yan Najeriya na fama da matsanancin talauci, hakan yasa basu iya siyan kaya.

Mutane kadan a Najeriya ke iya siyan sabuwar mota. Kasuwar sabbin motoci a Najeriya bata ci. Kamfanonin sun fi yadda da Ghana inda suka tattara komatsansu suka tare.

Volkswagen, Suzuki, Toyota, Nissan duk sun bude kamfanoninsu a Ghana.

Google ta bude dakin gwajin AI na farko a Afrika a Ghana

A 2019, Google ta sanar da wannan babban cigaban da ta samar tare da kafa shi a garin Accra. Wannan lamarin yasa an dinga tambayoyin cewa me yasa Ghana, duk da har a yau bata fadi dalilinta ba.

Saukin yin kasuwanci

Ko kun san cewa a duk fadin Afrika Najeriya ce kasar da ta fi wahalarwa kafin a yi wa kadara rijista? A dukkan kasashe 48, Najeriya ce ta 48 a saukin yin kasuwanci a Afrika.

Riga-kafin cutar korona duk ya tafi Ghana

Da yawa daga cikin siyasa da diflomasiyyar kasa da kasa da kuma makomarta ta dogara ne da yadda sauran duniya ke kallon kasar.

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2021, Ghana ta zama kasa ta farko a Afrika da ta samu riga-kafin COVAX na COVID-19.

Obama ya share Najeriya, ya ziyarci kasar Ghana

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasar Amurka, masu kiyasi sun dinga tunanin Najeriya zai fara kai ziyara, amma sai ya basu mamaki inda ya garzaya Ghana a 2009.

Duk da hakan ba komai bane, har Barack Obama ya bar mulkin Amurka, bai taba ziyartar kasar Najeriya ba.

Nasara mai cike da tarihi: Obasanjo da Kofi Anan

Ko kun san tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya so zama sakataren majalisar dinkin duniya a 1991?

Obasanjo ya fadi warwas a yunkurin da yayi na zama bakar fata dan Afrika na farko da zai zama sakataren majalisar dinkin duniya.

Abinda Obasanjo ya so, duk Kofi Anan ne ya samu kuma ya kafa babban tarihi.

KU KARANTA: Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar mata masu zaman kansu mazauna jihar

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng