Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe

Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe

- 'Yan sanda a jihar Imo sun kame tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha da yammacin jiya

- 'Yan sandan sun kama shi ne yayin wani rikici a wani otal din da aka rufe kwanakin baya

- An jiwa masu gadin otal din rauni, yayin da jama'ar Okorocha ke kokarin fasa otal din don shiga

An kama tsohon Gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, bayan da ya kuskura ya tamkawa Gwamna Hope Uzodimma don sake bude Royal Palm Estate da Gwamnatin Jihar ta garkame, Daily Trust ta ruwaito.

Tare da rakiyar surukinsa, Uche Nwosu, tsohon Gwamnan ya karya makullin da aka garkame otal din, wanda yake mallakar matar sa, Nkechi.

An ruwaito cewa Okorocha ya kutsa kai cikin otal din ne a fusace a ranar Lahadi, yana neman a ba shi damar shiga amma jami’an tsaron da ke kasa sun ki bude kofar.

KU KARANTA: Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri

Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe
Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe Hoto: The Nation
Asali: UGC

Jim kaɗan bayan haka, wasu hadiman gwamna Hope Uzodinma da aka ambata da suna Chinasa Nwaneri da Eric Uwakwe suka isa wurin tare da ‘yan sanda waɗanda suka kama Sanatan bayan sun fi karfin mutanensa a wurin.

Hakanan an kame Ijeoma Igboanusi, wani mataimakin shugaban ma’aikata a lokacin da Okorocha ke gwamna, da Lasbrey Okafor-Anyanwu.wanda ya kasance Kwamishina a gwamnatin Okorocha.

An ce mutane biyu sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka a lamarin.

Sanatan da wadanda aka kama tare da shi a halin yanzu ana tsare da su a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), Owerri.

KU KARANTA: Yanzun nan: Gwamnatin Niger ta samu nasarar kubutar da fasinjoji da 'yan fashi suka sace

Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe
Da dumi-dumi: An kama Sanata Okorocha da laifin bude wani otal din da aka rufe Hoto: The Nation
Asali: UGC

An ce dan majalisar da ke wakiltar gundumar sanata mai wakiltar Imo ta Yamma ya umarci mutanensa da su ba shi hanya ya shiga wurin sannan suka bude kofofin.

Bisa umarnin Okorocha, an bude kofofin amma bayan da mutanensa masu dauke da makamai suka lalata motoci tare da raunata masu tsaron wurin.

A wani labarin daban, Bayan fada tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar Shasha da ke Ibadan, asarar ta ratsa kabilun biyu; hatta shugabanni a cikin al'umma sun yi asarar da ta wuce lissafi.

Amma mako guda bayan mulkin tashin hankalin, kabilun biyu sun taru a karkashin rufi daya don yin sallar jam'i ta Juma'a aranar Juma'a.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel