Bayan Buhari ya gama mulki, APC za ta iya shan kashi a zaben da za ayi a 2023 inji Jigon Jam’iyya

Bayan Buhari ya gama mulki, APC za ta iya shan kashi a zaben da za ayi a 2023 inji Jigon Jam’iyya

- Shugaban kungiyar Progressive Governors’ Forum ya gargadi Shugabannin APC

- Salihu Lukman ya ce idan aka yi wasa, to APC ba za ta cigaba da mulki a 2023 ba

- Jigon jam’iyyar ya bayyana abin da ya jawo faduwar majalisar Adams Oshiomhole

Darekta Janar na kungiyar Progressive Governors’ Forum, Salihu Lukman, ya ja kunnen jam’iyyarsu ta APC, ya na mai kira da su yi hattara da 2023.

Punch ta rahoto Alhaji Salihu Lukman ya na cewa APC ta na nuna makauniyar soyayya ga wasu shugabanninta, har a kyale su, su yi abin da su ka ga dama.

Salihu Lukman ya gargadi jam’iyyar da cewa idan ta yi sake, ba za ta yi nasarar cigaba da mulkin Najeriya bayan wa’adin Muhammadu Buhari ya kare ba.

KU KARANTA: Ana neman dawo da Adams Oshiomhole kan kujerarsa - Salihu Lukman

Lukman ya fitar da jawabi a ranar Litinin, ya na tuna wa APC yadda ta rasa zaben gwamnoni a wasu jihohi a 2023 saboda sabanin cikin gida da zagon-kasa.

A dalilin haka, Lukman ya yi kira ga shugabannin APC su rika sa ido a kan ‘ya ‘yan jam’iyyar, musamman wadanda aka zaba su wakilci al'umma a Najeriya.

Darektan na PGF ya bada shawarar ayi hankali da wadanda ake gayyato wa cikin tafiyarsu, ya bada shawarar ayi masu horo na musamman idan sun shigo APC.

Shugaban kungiyar PGF yayi kira ga jam’iyyar mai mulki ta dauki darasi a kan yadda Adams Oshiomhole ya shugabanci APC tsakanin shekarar 2018 da 2020.

KU KARANTA: Oshiomhole ya zargi wasu gwamnoni da kokarin kai shi kasa a APC

Bayan Buhari ya gama mulki, APC za ta iya shan kashi a zaben da za ayi a 2023 inji Jigon Jam’iyya
Manyan Jam’iyyar APC a taro
Asali: Facebook

A cewar Lukman, da ace Adams Oshiomhole da majalisarsa sun rika gudanar da zabe a kai-a kai yadda ya dace, da watakila har yanzu ya na nan a kan kujerarsa.

Alhaji Lukman ya ce irin wannan makauniyar soyayya ce ta jawo rabuwar kai a APC, a karshe hakan ya jawo masu asara a 2019, ya ce dole ayi gyara kafin 2023.

A ranar Litinin kun ji cewa Abdulaziz Yari ya gargadi Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Matawalle game da hadarin barin PDP ya koma jam'iyyarsu ta APC.

Alhaji Abdulaziz Yari ya bayyana cewa wasu manyan APC su na zuga gwamna Matawalle ya shigo Jam’iyyar APC, wanda hakan zai jawo ya tashi a tutar babu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel