Mikel ya sha gaban Ighalo da Ahmed Musa a sahun gawurtattun Attajiran ‘Yan wasa 10

Mikel ya sha gaban Ighalo da Ahmed Musa a sahun gawurtattun Attajiran ‘Yan wasa 10

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ‘dan wasan Super Eagles, Mikel Obi shi ne Tauraron da ya fi kowane ‘dan kwallon Najeriya kudi a halin yanzu.

Mikel Obi mai shekaru 33 ya ba Naira biliyan 23 baya. ‘Dan wasan tsakiyar na kungiyar Stoke City ya buga wa Tianjin TEDA bayan ya bar Chelsea a 2017.

‘Dan wasa na biyu a jerin attajiran shi ne tsohon ‘dan wasan Inter Milan da Newcastle, Obafemi Akinwunmi Martins wanda ya mallaki Naira biliyan 14.

Obafemi Martins wanda aka rika yi wa lakabi da Obagoal ya na gaban Odion Jude Ighalo.

BBC Pidgin ta ce ‘dan wasan gaban na Wuhan Zall ya mallaki fiye da Dala miliyan 25 da kuma manyan gidaje a Legas da Italiya da dirka-dirkan motoci.

KU KARANTA: Abin da ya sa Ahmed Musa ya bar Al Nasr a Kasar Saudi

Ana hasashe ‘dan wasa Odion Jude Ighalo mai shekara 31 ya na da akalla Naira biliyan 12. Bayan barin Ingila, Ighalo ya na buga wa Al Shabab ta Saudi Arabia.

Har tsohon ‘dan wasan na Shanghai Shenhua da Man United ya ci wa kungiyar ta sa kwallaye uku.

Wanda ya rufe sahun farko shi ne tsohon mai tsaron ragar Super Eagles, Vincent Enyeama. Ragowar taurarin su ne irinsu: Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho.

An kawo jerin attajirai 10 na farko a shafin clacified.com

Mikel ya sha gaban Ighalo da Ahmed Musa a sahun gawurtattun Attajiran ‘Yan wasa 10
Obafemi Martins Hoto: Obagoal
Asali: Instagram

KU KARANTA: Tsohon 'dan wasan Super Eagles, Sofoluwe, ya rasu

1. John Obi Mikel - ₦23bn

2. Obafemi Akinwunmi Martins - ₦14bn

3. Odion Jude Ighalo - ₦12bn

4. Vincent Enyeama - ₦10bn

5. Victor Moses - ₦7.3bn

Ragowar sun hada da:

6. Ahmed Musa - ₦6.5bn

7. Emmanuel Emenike - ₦6.4bn

8. Victor Anichebe - ₦6bn

9. Kelechi Iheanacho - ₦1.4bn

10. Alex Iwobi - ₦1.3bn

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel