A karshe: Fayose ya saduda, ya kawo karshen rigimar da aka dade ana fama da ita a PDP

A karshe: Fayose ya saduda, ya kawo karshen rigimar da aka dade ana fama da ita a PDP

- Ayodele Fayose ya yi mubaya’a ga tsohon Gwamnan Oyo, Seyi Makinde

- Tsohon Gwamnan na Ekiti ya zabi ya yi aiki tare da Gwamnan jihar Oyo

- An dade ana ta kai ruwa rana PDP tsakanin magoya bayan ‘Yan siyasan

A ranar Litinin, 12 ga watan Afrilu, 2021, tsohon gwamna Ayodele Fayose, ya yi na’am da mai girma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin shugabansa.

Jaridar The Cable ta bayyana cewa a karon farko Ayodele Fayose ya yarda cewa Injiniya Seyi Makinde shi ne jagoran jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso yamma.

Tsohon gwamna Ayodele Fayose ya bayyana Seyi Makinde a matsayin jagoran PDP ne a wajen zaben shugabannin jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Litinin.

KU KARANTA: Ana harbe-harbe wajen zaben Shugabannin PDP

Wannan mataki da Fayose ya dauka na sallama wa gwamna Makinde jam’iyyar PDP ya kawo karshen rigimar da aka dade ana fama da ita a Kudu maso yamma.

Wannan rigima ta yi sanadiyyar da manyan ‘yan siyasar su ka fito da takara dabam-dabam a zaben shugaban jam’iyyar PDP na reshen Kudu maso yammacin Najeriya.

A karshe shugabannin PDP sun yi nasarar sasanta gwamnan na Oyo da tsohon gwamnan jihar Ekiti, inda Fayose ya ajiye kayan fada, ya nemi afuwar ‘yan jam’iyyarsa.

“Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ‘danuwana ne, aboki na, kuma shugabanmu.” Fayose ya furta wadannan kalamai wajen zaben PDP jiya a garin Osogbo, jihar Osun.

A karshe: Fayose ya saduda, ya kawo karshen rigimar da ake dade ana fama da ita a PDP
Fayose da Makinde Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: “Kai kuma a wa?” – Manyan ‘Yan Jam’iyya sun juya Akpabio baya a A/Ibom

“Zaben nan ya zo da wannan irin yanayi, ana tambayar wanene shugabanmu, Gwamna Seyi Makinde shi ne shugabanmu. Don haka ka da a raba kanmu” inji Fayose.

Ayo Fayose ya ce shi da Makinde duk abu daya ya yi su. “Duk inda ya shiga, zan shiga.” A karshe jigon adawar ya bukaci mutane su yafe masa a dalilin sabanin da ya jawo.

An dade ana rikici tsakanin Ayo Fayose da Seyi Makinde game da wanda ke da iko da PDP a yankin, har Fayose ya fito ya na jan-kunnen Gwamnan mai shekara 53.

Yayin da wasu su ke tare da Makinde wanda shi kadai ne gwamnan PDP a yankin, wasu sun yi mubaya’a ne ga Ayo Fayose wanda ya ke ganin gwamnan ba kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel