Akwai aiki: Tsohon Sarki Sanusi II ya koka game da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ta ke ci

Akwai aiki: Tsohon Sarki Sanusi II ya koka game da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ta ke ci

- Tsohon Sarkin Kano ya ce bashin da ke kan Najeriya ya karu sosai a shekara 10

- Muhammadu Sanusi ya ce nauyin bashin Gwamnati ya tashi daga 8% zuwa 400%

- Sanusi II ya soki tsarin da ake bi na auna iya biyan bashi da karfin tattalin arziki

Muhammadu Sanusi II ya ce alkaluman kason bashin wajen Najeriya da kudin da kasar ta ke samu ya tashi da sama da 400% daga shekarar 2011 zuwa 2020.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da ya ke wani bayani a ranar Alhamis, tsohon gwamnan na bankin CBN, ya koka a kan kudin da ake bin Najeriya bashi.

Sanusi Lamido Sanusi kamar yadda aka san shi a baya ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi magana da shi a wata tattaunawa da Heinrich Böll ta shirya.

KU KARANTA: Muddin ka na cin mutuncin Kwankwaso, babu ni babu auren ka - Budurwa

Malam Muhammadu Sanusi II ya ce alkaluman CBN sun nuna cewa kudin shigan da aka samu daga haraji a Najeriya a 2011 ya kai kusan Naira tiriliyan 19.

Sanusi II ya ce a wancan lokaci duka-duka bashin da ake bin Najeriya bai zarce 10% na kudin da kasar ta ke samu ba, sai dai yanzu, ya ce lamarin ya sake zani.

“Zuwa 2020, kasashen waje na bin mu bashin kusan $33.4b, kuma abin da mu ka iya samu a 2020 kusan $8.3b ne, mun tashi daga 8% a 2011, zuwa 400% a 2020.”

Tsohon Sarkin na Kano ya ce alkaluma sun nuna cewa Najeriya ta na cikin hadarin bashi, musamman ganin yadda kudin da ake samu daga mai ya ke yin kasa.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Gwamna ya dauke motocin Gwamnati ya yi gaba

Tsohon Sarki Sanusi II ya koka game da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ta ke ci
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
Asali: UGC

Malam Sanusi II ya yi fatali da tsarin da gwamnati ta ke bi wajen aro kudin na alakanta nauyin bashi da kuma karfin tattalin arziki na GDP, ya ce hakan shirme ne.

“Ba da karfin tattalin arzikin kasa ake biyan bashi ba, ana biyan bashi ne da kudin shiga.” Inji Sanusi II.

Masanin tattalin arzikin ya ce karfin biyan bashi ba a GDP yake ba, ya ce idan mafi yawan mutane ba su biyan haraji, gwamnati za ta iya fada wa cikin taurin bashi.

Kwanakin baya aka ji Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan dambarwar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnati da kuma malaman jihar Kano.

Muhammadu Sanusi II ya fito ya nuna rashin goyon baya ga da’awar Abduljabbar Nasiru Kabara, ya yi kira ga al’ummar Kano su rike koyawar Shehu Usman Danfodio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel