Gwamnatin Najeriya ta yi gum game da lokacin da Shugaba Buhari zai iso gida

Gwamnatin Najeriya ta yi gum game da lokacin da Shugaba Buhari zai iso gida

- Babu wanda ya san ainihin lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo

- Ministan yada labarai ya ki bada amsa game da ranar dawowar Shugaban kasa

- Lai Mohammed ya ce abin da ke gaban gwamnati yanzu shi ne matsalar tsaro

Da alamu dai sai mai Allan-musuru ne zai iya sanin ranar da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya.

Kawo yanzu ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021, babu wanda ya san takamaimen lokacin da shugaban Najeriya zai baro kasar waje.

Da aka tambayi Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed, a game da wannan batu, bai iya bada wata gamsasshiyar amsa ba.

KU KARANTA: Boko Haram: Ba za mu iya cewa komai game da Pantami ba - FBI

Jaridar The Nation ta ce manema labarai sun jefa wa Alhaji Lai Mohammed wannan tambaya ne dazu a fadar Shugaban kasa na Aso Villa.

Mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari, ya yi alkawari cewa shugaban kasar zai dawo Najeriya ne a cikin mako na biyu na Afrilu.

Ganin cewa an kai wannan lokaci, manema labarai su ka nemi jin ta bakin Ministan labaran kasar, amma sai ya yi ta yi masu kewaye-kewaye.

An rahoto Lai Mohammed ya ce: "Yau Laraba, makon nan zai kare ne a ranar Asabar. Saboda haka menene wani abin surutu a game da wannan.”

KU KARANTA: Mu na cikin hadarin katutun bashi a Najeriya inji Sanusi II

Gwamnatin Najeriya ta yi gum game da lokacin da Shugaba Buhari zai iso gida
Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed
Asali: UGC

A cewar Ministan, gwamnatin tarayya ta fi maida hankali a kan matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a kan lokacin dawowar shugaban kasa.

Har yanzu dai ana sa ran cewa shugaba Muhammadu Buhari zai dawo bakin aiki ne a makon nan, ganin ya shafe kwanaki har 15 a birnin Landan.

Ba wannan ne karon farko da shugaban kasar Najeriyar ya je ganin Likitocinsa a kasar waje ba.

Kwanakin baya ku ka ji cewa wasu 'yan kasar nan mazauna Birtaniya sun gudanar da zanga-zanga domin yin tir da zaman da Buhari ya ke yi a Landan.

Masu zanga-zangar sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel