Wasu ‘Yan bindiga sun tare titi da rana, sun sace fasinjoji rututu a mota a Katsina
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fasinjoji a hanyar Katsina a ranar Lahadi
- Rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da matafiya 15 da rana tsaka jiya
- Jami’an tsaro sun musanya adadin da aka bada, sun ce har an ceto wasu mutane
Katsina Post ta ce akalla fasinjoji 15 da su ke tafiya a wata mota mai lamba KZR 345ZT aka yi awon-gaba da su a karamar hukumar Safana, jihar Katsina.
Jaridar ta bayyana cewa wannan mummunan lamari ya auku ne a hanyar Tsaskiya-Ummadau da ke garin Safana a jiya, ranar Lahadi, 11 ga watan Afrilu, 2021.
Ana zargin cewa miyagun ‘yan bindiga ne su ka auka wa wadannan fasinjoji, su ka yi garkuwa da su. Amma jami'an tsaro sun fara gano wasu daga cikinsu a jeji.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun karbe miliyoyi a hannun ayarin matafiya
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa wasu gungun mutane kusan 20 dauke da mugayen makamai su ka tare wata katuwar motar J5 da ta dauko fasinjojin.
Wanda ya san abin da ya faru, ya sanar da manema labarai cewa fasinjojin sun fito ne daga kasuwar Jibiya da ke shiyyar Arewacin jihar a kan iyaka da Nijar.
Malam Aliyu Rumawa ya bada labari cewa yayin da ‘yan bindigan su ka hango wannan mota, sai su ka shiga buda wuta ta ko ina domin su firgita ‘yan cikin motar.
Kamar yadda Aliyu Rumawa ya bayyana dazu, kiri-kiri wadannan ‘yan bindiga su ka dauke kimanin mutane 15 daga cikin fasinjoji 18 da su ke cikin motar ta J5.
KU KARANTA: ‘Yan kasuwa sun hararo saukar kudin man fetur a Najeriya
Mai magana a madadin ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce dakarun jami’an tsaro sun fara ceto wasu fasinjojin.
“Fasinjoji tara ne ba 15 ba. Abin da ya faru shi ne jiya (Lahadi) da kimanin karfe 3:30 na rana. ‘yan bindiga su ka sace mutum tara a motar J5 mai lamba KZR 345ZT.”
Ya ce: “Bayan abin ya faru, DPO ya jagoranci dakarun Operation Puff Adder, sun shiga jejin. Sun iya ceto mutane hudu daga cikin fasinjojin, sauran biyar su na tsare."
Kwanakin baya kun samu labari cewa a wani samame da 'yan bindiga su ka kai Katsina, an salwantar da rayukan wasu jami'ai 16 daga cikin sojojin Najeriya.
Daga cikin dakarun da su ka riga mu gidan gaskiya a karamar hukumar Jibiya har da wani babban jami'i da ya kai matsayin Manjo, Kyaftin, da kuma Laftana.
Asali: Legit.ng