Labari mai zafi: An kafa 'EBUBEAGU' saboda rashin tsaro a Imo, Anambra, Ebonyi, Enugu

Labari mai zafi: An kafa 'EBUBEAGU' saboda rashin tsaro a Imo, Anambra, Ebonyi, Enugu

- Gwamnonin Jihohin Kudu maso gabas sun yi zama a kan sha’anin tsaro

- An gudanar da wannan taro ne a garin Owerri, jihar Imo a ranar Lahadi

- A karshen wannan zama, jihohin sun kafa jami’an tsaronsu na musamman

Jihohin kudu maso gabas sun kafa jami’an tsaronsu na musamman a dalilin matsalolin da ake fuskanta na rashin tsaro a ‘yan kwanakin nan.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto cewa an sa wa wadannan jami’an tsaro da aka kafa suna da EBUBEAGU.

An dauki wannan mataki ne bayan gwamnonin yankin da sauran masu ruwa da tsaki sun yi wani zama na musamman a jihar Imo a ranar Lahadi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kona ofishin yan sanda a Imo

Gwamnonin jihohin Anambra, Abia, Ebonyi, Imo da Enugu da wasu manyan jami’an tsaro sun halarci wannan zama da aka yi a kan harkar tsaron.

Daga cikin wadanda su ka halarta akwai manyan sojojin sama da ruwan Najeriya, da kuma Sufeta-Janar na 'yan sanda da wakilan Ohanaeze Ndigbo.

Wannan taro ya zo ne kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun auka wa gidan yarin Owerri, inda su ka fito da mutane kusan 2, 000 da ke zaman kaso.

Bayan harin da aka kai a gidan yari, wadannan ‘yan bindiga sun dura ofishin ‘yan sanda a jihar Imo, inda su ka yi barna har da kona motocin jami’ai.

Labari mai zafi: An kafa 'EBUBEAGU' saboda rashin tsaro a Imo, Anambra, Ebonyi, Enugu
Taron Gwamnonin Kudu maso gabas Hoto: twitter.com/govhopeuzodinma
Asali: Twitter

KU KARANTA: SWAGA da BAT su na taya Asiwaju Tinubu yakin neman shugaban kasa

Ta shafinsa na Twitter, gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya fito ya yi bayanin abin da su ka tattauna a taron, ya ce sun kafa jami’an tsaro na EBUBEAGU.

Wannan bayani da mai girma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya yi, ya zo ne shekara daya bayan gwamnonin Yarbawa sun kafa Amotekun.

Akwai yiwuwar wannan yunkuri da gwamnonin su ke yi ya gamu da tasgaro ta fuskar doka domin gwamnatin tarayya ce ta ke da iko da sha’anin tsaro.

A makon da ya gabata kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun sake kai hari a wani ofishin 'yan sanda a Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, jihar Imo.

Rahotanni sun ce 'tan bindigan sun kai hari ne da misalin karfe 1:00 na dare, inda su ka fito da dukkannin wadanda su ke tsare da su a ofishin 'yan sandan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng