Sanata Shekarau zai shimfida titi a kauyen tsohon Gwamna Kwankwaso a jihar Kano

Sanata Shekarau zai shimfida titi a kauyen tsohon Gwamna Kwankwaso a jihar Kano

- Sanata Ibrahim Shekarau zai gina wani titi a karamar hukumar Madobi

- Tsohon Gwamnan Kano ya ce wannan ya na cikin ayyukan mazabarsa

- Abokin hamayyarsa, Rabi'u Kwankwaso, ya fito ne daga garin Madobi

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau zai shimfida titi a karamar hukumar Madabo, jihar Kano.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto cewa Sanata Ibrahim Shekarau zai yi titin da zai hada wasu kauyuka uku a cikin garin na Madobi.

Babban abokin adawar Ibrahim Shekarau watau tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito ne daga Madobi inda Sanatan ya kai wannan kwangilar.

KU KARANTA: Sauya-sheka: Malam Shekarau ya gana da Kwankwaso a Abuja

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa za ayi wannan titi a yankin Kauran Mata ne saboda a sama wa dinbin mutanen da su ke bin wannan hanya sauki.

Sanatan ya bayyana cewa wannan titi mai tsawon kilomita 1.5 ya na cikin ayyukan mazabun da aka ware masa a cikin kundin kasafin kudin shekarar 2020.

A cewar Ibrahim Shekarau, an ware kudi har Naira miliyan 200 domin ayi wannan muhimmin aiki.

“Wannan ya na cikin ayyukan da mu ke da su wadanda su na nan tafe, ba da dadewa ba, nan da wata daya ko biyu mu ke sa ran gwamnati ta fara fitar da kudin.”

Sanata Shekarau zai shimfida titi a kauyen tsohon Gwamna Kwankwaso a jihar Kano
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Siyasar Kano: Shekarau zai maye gurbin Kwankwaso a majalisar dattawa

“’Dan kwangilar ya sa lokaci na watanni 12, ya ce a cikin wannan wa'adi zai kammala aikin, ya tabbatar da cewa zai gama kwangilar kafin lokacin.” inji Shekarau.

Shekarau ya kuma bayyana cewa zai gina makarantar Kur’ani domin tuna wa da kakansa wanda ya rasu, marigayin ya kasance malamin addini da ya ke da rai.

‘Dan majalisar ya ce za a gina wannan makaranta ne daki-daki, ya ce a ciki za a samu wurin kwana.

A baya an ji tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya na cewa akwai ƙyakkyawar alaka tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Tsakaninsa da Sanata Kwankwaso, Malam Shekarau ya ce: "Akwai alaƙa ƙyakkyawa tsakanin mu. Banbancin mu na siyasa ba zai taɓa ɓata wannan alakar ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel