Rikici shakaf ya barke a APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun ki yi wa Ministan Buhari mubaya’a

Rikici shakaf ya barke a APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun ki yi wa Ministan Buhari mubaya’a

- Wasu ‘Ya ‘yan APC sun watsawa Godswill Akpabio kasa a cikin idanu

- ‘Yan jam’iyyar sun ce sam Sanata Akpabio ba shugabansu ba ne a APC

- Dr. Ita Udosen ba su tare da bangaren su Sam Ewang a jihar Akwa Ibom

Daily Trust ta ce wasu daga cikin manyan jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom ba su yi na’am da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugabansu ba.

A wajen taron da aka yi domin ayi sulhu, ‘ya ‘yan jam’iyyar sun nuna ba su tare da bangaren Sam Ewang da ya tsaida Godswill Akpabio a matsayin shugaba.

Wasu kusoshin jam’iyyar APC mai adawa a Akwa Ibom da ke tare da Sanata John Akpanuodehe, sun tabbatar da cewa ba su karkashin Godswill Akpabio.

KU KARANTA: Ana fada a kan komawar Gwamnan Zamfara APC

Sauran wadanda ke tare da John Akpanuodehe sun hada da Obong Umana Umana, hadimin shugaban kasa, Ita Enang, da shugaban NDDC. Efiong Akwa

A karshen wannan zama da aka yi, bangaren ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sun ce zaben Minista Neja-Deltan da aka yi a matsayin jagora a Akwa Ibom ya saba doka.

Dr. Ita Udosen da Austin Ekanem su ka sa hannu a madadin sauran ‘yan bangaren a wannan taron.

“Zaben Godswill Akpabio da aka yi a matsayin jagoran jam’iyya na jiha a haramtaccen taron da aka yi a ranar 28 ga watan Maris, ya ci karo da dokar APC.”

Rikici shakaf ya barke a APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun ki yi wa Ministan Buhari mubaya’a
Tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023

“Jam’iyya ta na tuna wa kowane ‘danta da sauran jam’a cewa shugaban jam’iyya (ko shugaban rikon kwarya) shi kadai ne doka ta sani a matsayin jagora.”

Ita Udosen da mutanensa sun kafa hujja ne da sashe 12.9 Sub (i) na tsarin mulkin jam’iyyar APC wanda aka yi wa garambawul a watan Oktoban shekarar 2014.

A karshen taron, ‘ya ‘yan jam’iyyar sun bayyana cewa babu wasu bangarorin taware a cikin APC, sannan aka yi kira ga kowa da kowa su zo a hada-kai a tafi tare.

Dazu kun ji cewa Salihu Lukman ya na ganin makauniyar soyayyar da ake yi wa shugabanni ta kai jam’iyyar APC, ta baro ta a zaben da ya wuce na shekarar 2019.

Shugaban na PGF ya ce kura-kuren da aka yi a baya za su iya jefa APC ga halaka idan aka yi sake nan gaba, ya yi kira ayi hattara da masu shigowa cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel