Rikicin Hijabi da nadin mukamai: Kiristoci sun maidawa Majalisar kolin addinin Musulunci martani

Rikicin Hijabi da nadin mukamai: Kiristoci sun maidawa Majalisar kolin addinin Musulunci martani

- Kiristoci sun fito su na zargin NSCIA da kare Gwamnatin Muhammadu Buhari

- Kungiyar CAN ta yi wa Majalisar NSCIA raddi a kan kalaman da ta yi kwanaki

- NSCIA ta wanke Gwamnatin APC daga zargin rashin adalci wajen nadin Alkalai

Kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta maida wa majalisar kolin addinin musulunci, NSCIA martani game da kalamanta a kan hijabi da nadin Alkalai.

Jaridar The Nation ta ce kungiyar CAN ta fitar da jawabi ta bakin sakatarenta na kasa, Joseph Daramola, ta na cewa musulmai sun mamaye bangaren shari’a.

CAN ta yi raddi ne bayan majalisar da mai alfarma Sarkin Musulmi yake jagoranta ta zargi CAN da yunkurin kawo rikici kan amfani da hijabi a jihar Kwara.

KU KARANTA: Malamin Musulunci ya sa Dalibai sun lakadawa Yaro dukan da ya kusa mutuwa

Kungiyar kiristocin ta ce NSCIA ta yi amfani da maganganu marasa dadi wajen sukar ta a kokarin kare rashin adalcin da ake yi wajen nada mukamai a gwamnati.

Joseph Daramola ya ce bayan bangaren shari’a, musulmai ne su ka mamaye bangarorin majalisa da masu zartar wa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Daramola a madadin CAN ya zargi majalisar kolin addinin musulunci da zama lauyan da ke kare rashin adalci da raba kai da gazawar gwamnatin APC mai-ci.

“Mun so ace NSCIA ta kyale gwamnatin nan ta fito ta kare kanta da kanta.” Inji Joseph Daramola.

KU KARANTA: Mamman Daura ya bayyana a Yola bayan doguwar kusufi

Rikicin Hijabi da nadin mukamai: Kiristoci sun maidawa Majalisar kolin addinin Musulunci martani
Buhari da manyan kungiyar Kiristocin NAN
Asali: UGC

CAN ta yi wa Majalisar Sarkin Musulmai raddi a kan nadin Alkalin kotu a Najeriya

“Mun san yadda aka tsige Alkalin alkalai Walter Onnoghen ba tare da bin doka ba. Ba don irinsu Umar Dangiwa ba, da ba a kyale Monica Dongban-Mensem ta dare kujerarta ba.”

Kungiyar CAN ta hakikance a kan cewa ba a dama wa da kiristoci a majalisar tsaro ta kasa, alhali tsarin mulkin kasa ya bukaci gwamnatin tarayya ta rika tafiya da kowa da kowa ne.

CAN ta kalubalanci gwamnatin tarayya ko masu magana da yawunta su wallafa sunayen duk wadanda aka ba mukamai tun daga 2015 da kuma asalin jihohin da su ka fito.

A watan jiya ne a aka ji cewa Majalisar shari'a ta tarayya NJC a karkashin jagorancin babban Alkalin Alkalai na kasa IT. Muhammad CFR,ta nada sababbin manyan Alkalai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel