Da duminsa: Fulani makiyaya sun kai hari yankin Ngbo dake Ebonyi

Da duminsa: Fulani makiyaya sun kai hari yankin Ngbo dake Ebonyi

- Labari da ke zuwa a halin yanzu shine na farmakin da makiyaya suka kai yankin Ngbo dake karamar hukumar Ohaukwu

- Mugun farmakin ba-zatan ya auku ne da sa'o'in farko na ranar Litinin, 12 ga watan Afirilun 2021

- An gano cewa rayuka masu tarin yawa sun salwanta kuma gidajen jama'a da yawa sun babbake

Rahotannin dake samun Vanguard a halin yanzu sun nuna cewa Fulani makiyaya tun a sa'o'in farkon ranar Litinin suka kai farmaki kauyen Ngbo dake karamar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi.

An tattaro cewa mutane da yawa sun rasa rayukansu sakamakon wannan cigaban inda gidajen jama'a da basu da laifin zaune balle na tsaye suka babbake a yankin.

A ranar Laraba ta cikin makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Ebonyi ta bada ladubban tsari na kungiyar 'yan sa kai ta mutum 1,000 a fadin jihar.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari ma'adanar kayan tallafi, sun kone wurare a Borno

Da duminsa: Fulani makiyaya sun kai hari yankin Ngbo dake Ebonyi
Da duminsa: Fulani makiyaya sun kai hari yankin Ngbo dake Ebonyi. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak

Harin, wanda aka kwatanta da na ba-zata, ya shafi kauyen Ebele dake yankin Umuogodoakpa yayin da wasu wadanda lamarin ya faru dasu suke shan iska a cikin gidajensu.

Idan za a tuna, makiyayan sun kai hari yankuna hudu na karamar hukumar Ishielu inda suka kashe sama da mutum 25, kisan wulakanci.

A yayin rubuta wannan rahoton, ba a kama ko daya daga cikin wadanda ake zargi ba.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD da wasa da rayukan al'umma a wannan halin da kasa take ciki na tsanani.

Dr Chris Ngige, wanda shine ministan ayyuka da kwadago, ya jefa wannan zargin garesu ne a ranar Juma'a da suka shiga taro da likitocin a Abuja, babban birnin tarayya.

Ya ja kunnen 'yan kungiyar inda ya jefa wannan zargin a garesu inda yace suna kokarin fifita jindadi da walwalarsu sama da rayukan al'umma.

A cewarsa NARD ko kuma NMA kungiyace ta kasuwanci kuma 'yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu sakamakon wannan yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: